Dantsoho Ya Kaddamar Da Aikin Tsaftace Tashar Jirgi Ta Tin-Can Island
Published: 31st, May 2025 GMT
“Ya zamar mana wajbi, mu kulla wannan hadakar, musamman domoin mu tabbatar da cewa, mun tsaftace tsarin,” Inji Dantsoho.
Ya kara da cewa, wannan aikin, ba wai kawai za kara habaka samar da kariya da kuma kara ingnata tsaro bane, har da kuma bayar da gagarumar gudunmawa, wajen kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.
A cewar Shugaban, cunkoson da ake samu a Tashar ta Tin Can Island na ci gaba da haifar da jinkiri da rashin gudanar da ayyuka yadda suka kamata da kuma rage gudanar da hada-hadar kasuwanci, yadda ta kamata, wanda kuma hakan, ke janyowa kara habaka tattalin arzikin kasar.
Dantsoho wanda Babban Janar Manaja na sashen kula da tsaro a Hukumar ta NPA Mista Anthony Edosomwan ya wakilce shi a wajen kaddamar da aikin ya bayyana cewa, za a gudanar da aikin ne, zuwa kwana uku, musamman domin a samu nasarar gudanar da aikin.
Shugaban ya kara da cewa, sashen kula da tsaro na Hukumar ya wallafa a kafafen yada labarai, kan sanarwar wayar da kan jama’a kan batun mahimmancin, tsaftace Tashar ta Tin Can Island.
“Wannan wani mataki ne, da aka samu goyon bayan masu ruwa da tsaki ciki har da masu yin amfani da Tashar da ‘yan kasuwa da kuma sauran alummar da ke a kusa da yankin”, A cewar Dantsoho.
Shugaban ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA ba za ta yi kasa a guiwa, wajen kara mayar da hankali da kuma zagewa, domin ta samu cin nasara wajen tabbatar da tsaftace muhalli da kuma samar da kyakyawan yanayi, a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar ba.
“Yanayi na samun gurbatacciyar Iska da kutsen da ake yiwa Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, abu ne da Hukumar ta NPA, ba za ta rungume hannu ta bari ba, ” Inji Dantsoho.
“Wannan aikin na tsafrace Tashar ba wai kawai na da alfanu ga ayyukan da ake gudanarwa a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar bane, hatta alumomin da suke daura da Tashoshin, suma zai yi masu alfanu,“ A cewar Shuaban .
Shuaban ya kara da cewa, sashen kula da tsaro na Hukumar ta NPA da faro shi a wannan shekarar ta 2025, na daga cikin shiryae-shiryen rage cunkoso da kuma samar da saukin gudanar da ayyuka, Hukumar ta NPA, wanda hakan zai taimaka matuka wajen samar da kyakywar makoma ga Tashoshin Jiragen Ruwa, da ke a daukacin kasar nan.
A cewar Shugaban, wannan hadakar da sauran jami’an tsaro da kuma yin gangamin na wayar da kan alumma, Hukumar na bukatar goyon bayan alumma, dominn ta samu nasarar, aikin da ta sanya a gaba,
“A saboda haka, Mahukuntan Hukumar ta NPA, na bukatar goyon baya da hadin kan jama’a musamman domin a samar da kyakyawan yanin da ya dace a Tashar Jirgin Ruwan,” A cewar Shugaban.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Tashoshin Jiragen Hukumar ta NPA
এছাড়াও পড়ুন:
An kaddamar Da Wani Shiri Na Ba ‘Yan Mata 200,000 Tallafin Audugar Mata A Kano
An shawarci mata da su daina amfani da tsumma ko soson katifa, da takarda a lokacin al’adar su don inganta tsafta da rigakafin matsalolin lafiya.
Jami’ar tallafawa masu kula da tsaftar jinin haila a jihar Kano (MH-NoW) Amina Sabiu Musa ta yi wannan kiran ne a lokacin wani taron karawa juna sani na tsaftar jinin haila ga kwararrun ‘yan jarida da masu fada a ji a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Kano.
A cewarta, shirin na MH-NoW ya shafi ‘yan mata da mata masu shekaru 10 zuwa 24 su 200,000 da nufin magance matsalar talaucin kudin sayen audugar mata a fadin Najeriya.
Ta bayyana cewa shirin wanda Population Services International (PSI) Nigeria ta aiwatar, zai hada da masu raba kayan aikin tsaftar muhalli da za a sake amfani da su don taimakawa wajen rage radadin talauci a wannan banagen.
“Ana gudanar da aikin a wasu jahohin Najeriya, tare da mai da hankali kan dalibai da mata matasa a al’ummomi 15 dake fadin kananan hukumomin Ghari, Tsanyawa, da Nasarawa a Kano,” in ji Amina.
Shima da yake jawabi a wajen taron, mataimakin daraktan bincike da kididdiga na ma’aikatar mata, yara da masu bukata ta musamman ta jihar Kano, Alhaji Zubair Abdulmumin Zubair ya bukaci iyaye da su ba da fifiko ga tsaftar jinin haila ta hanyar samar da kayan tsafta da kuma jagoranci mai kyau ga ‘ya’yansu mata.
Ya nuna damuwarsa kan rahotannin da ke cewa dalibai mata da yawa ba sa zuwa makaranta a lokutansu sakamakon rashin samun kayayyakin tsaftar muhalli da kuma rashin audugar mata a lokacin al’ada.
Ya yi kira ga maza, iyaye, maza da mata da duk masu ruwa da tsaki da su yi watsi da tatsuniyoyi masu cutarwa game da jinin haila tare da tallafawa ilimin haila.
“Dole ne kuma a ilmantar da maza game da jinin haila don su fahimci sauyin yanayi da yanayin da mata ke fuskanta a lokacin al’ada,”
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka zanta da gidan rediyon Najeriya Aminu Abdullahi da Hannatu Sulaiman Abba da kuma Maimuna O. Yusuf sun bayyana taron da ya dace.
A matsayinsu na masu yada labarai, sun yi alkawarin ba da horo ga wasu kuma za su yi amfani da dandamali daban-daban na don Magana akan haila.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa taron bitar ya samu halartar dimbin mahalarta.
Khadija Aliyu