Masu Bincike Na Sin Sun Cimma Sabon Sakamako A Fannin Saurin Sadarwa Tsakanin Tauraron Dan Adam Da Doron Duniya
Published: 28th, May 2025 GMT
Wasu masu binciken fasaha na kasar Sin, sun cimma sabon sakamako a fannin saurin sadarwa tsakanin tauraron dan adam da doron duniya, inda suka karya matsayin saurin da ake da shi a baya, ta amfani da salon X-band mai tasha guda.
Rahotanni na cewa masu binciken, daga cibiyar binciken harkokin sadarwar samaniya ko AIR, karkashin hukumar lura da binciken kimiyya ta kasar Sin, sun cimma nasarar gudanar da sadarwa da saurin da ya kai megabit 2,100 duk dakika, adadin da ya haura wanda ake iya samu ta fasahar “microwave”, da karin kaso 75 bisa dari na saurin sadarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
Gwamnatin Jihar Yobe ta ƙaddamar da shirin fara amfani da ma’adinan ƙarƙashin ƙasa da Allah SWT ya hore ma ta da nufin haɓaka tattalin arzikinta tare da samarwa al’umma aikin yi.
A yayin ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na Jihar da aka yi a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Jihar da ke Damaturu, Gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya ce kamfanin haɓaka ma’adanai ta Yobe Limited ita ce kawai hukumar da aka bai wa izini don gudanar da duk ayyukan bincike da haƙar ma’adinai a faɗin jihar.
Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFAYana mai cewa, kamfanin haƙar ma’adinai na Yobe a halin yanzu shi ne, ƙashin bayan da zai samarwa Jihar hanyoyin dogaro.
“Jihar Yobe tana da wadataccen albarkatun ma’adinai kamar: Limestone, gypsum, kaolin, granite, Quartz, silica da sauran su duk da haka, tsawon shekaru da yawa, waɗannan ma’adinai sun kasance ba a amfani da su sosai kuma a yanzu lokaci ya yi da za a mayar da waɗannan ma’adinai da aka ɓoye zuwa kadarorin da za su samar da ayyukan yi, samar da wadata da kuma ciyar da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na mutanenmu gaba ɗaya.”
“Manufarmu ita ce tsara wani tsari don ci gaban fannin haƙar ma’adinai a Jihar Yobe ta hanyar da ta dace da manufofin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da haɗa kan al’umma, jawo hankalin masu zuba jari masu aminci da kuma tabbatar da alhakin gyara muhalli.
“kuma mun yi imanin cewa haƙar ma’adinai idan aka sarrafa shi yadda ya kamata, zai iya zama babban abin da ke haifar da juriyar tattalin arzikin jiharmu, samar da aikin yi ga matasa da kuma samar da kuɗaɗen shiga.”
“Muna hasashen samar da fannin haƙar ma’adinai wanda zai iya aiki a cikin tsarin dokoki, wanda ke tabbatar da ɗorewar muhalli da fa’idar al’umma; wanda ke haɗaka da haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu waɗanda aka amince da riƙon amana; wanda ke jawo hankalin masu zuba jari na ƙasashen waje.” Cewar Gwamna Buni.