2025-11-26@22:54:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8084

«a aiwatar da»:

    Daga Isma’il Adamu  Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar. Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace. Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa...
    An naɗa Andrea Thompson, ’yar ƙasar Birtaniya, a matsayin mace mafi ƙarfi a duniya. Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da cewa wanda aka bayyana a matsayin zakara — Jammy Booker — tun da farko namiji ne da aka sauya masa halitta zuwa mace, lamarin da ya sa aka soke nasararsa bisa saɓawa dokokin gasar. Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Thompson mai shekaru 43, ta karɓi lambar yabon ne daga masu shirya gasar nunin ƙarfi ta duniya, kwanaki biyu bayan kammala bikin a Arlington da ke birnin Texas na Amurka, wanda aka gudanar a daga 20 zuwa 23 ga watan Nuwamba. Gasar nuna ƙarfin ta...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan. Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000. Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu Haka kuma, Tinubu...
    Rahotanni sun bayyana cewa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun kashe akalla yan mata 33000 a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar Gaza. Ma’aikatar fa fitar da wannan sanarwar ce a wajen taron ranar kawo karshen hare-hare kan mata ta duniya . kuma tayi kaca-kaca da gwamnatin sahayuniya game da irin muggan laifukan yaki da ta tafka, inda ta rika amfani da makamai na zamani kan alummar falasdinu Kididdigar ta nuna cewa sama da mata 12500 da kuma yara 20,000 ne Isra’ila ta kashe a harin da ta kai tun daga watan oktoban shekara ta 2023. Har ila yau ma’aikatar ta bayyana cewa lallai a kwai...
    A yammacin nan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a ci gaba da Gasar Zakarun Turai, duk da rashin wasu manyan ’yan wasanta biyu. Babban mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtois, da ɗan wasan baya Dean Huijsen, na fama da jinya, lamarin da zai hana su buga wannan muhimmin wasa. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu Yanzu haka jerin ’yan wasan Madrid da ke jinya sun haɗa da: Thibaut Courtois, Dean Huijsen, Antonio Rüdiger, David Alaba, Franco Mastantuono, da Éder Militão. Tun bayan zuwan sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso, Courtois ya riƙe ragamar tsaron raga a dukkan wasanni 17 da suka buga a...
    Jakadan kasar Aljeriya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi tir da abin da ya kira zalunci isra’ila da kuma ci gaba da kai hare-hare kan mutane kasashen labanon, Syria, da Gaza da kuma gabar yammacin kogin jodan , yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki mataken gaggawa wajen dakatar da wadannan hare haren, kuma akwai dubban laifuffukan da Isra’ila ta aikata da ba’a manta ba kuma ba’a dauki wani mataki a kai ba. Aljeriya ta yi wannan bayanin  ne bayan karuwar sukar da ake yi a kwamitin tsaro game da mataken da isra’ila ke dauka a daidai lokacin da ake cikin matsala game da isar da taimakon agaji ga alummar gaza. A taron da kwamitin tsaro...
    Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu dauke da makamai sun kama shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo a yau Laraba, kwanaki uku bayan da aka yi zaben shugaban kasa. Rahotannin sun ce an yi ta harbe harbe a babban birnin kasar, a yayin da Alummar kasar ke zaman jiran sakamako zagaye na farko na zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi. Zuwa yanzu ba a tabbatar da ko su wane ne suka yi harbin ba. Rahotannin sun kuma ce an yi ta harbe harben a kusa da fadar shugaban kasar da ofishin hukumar zabe a yau Laraba, inda mutane suka tarwatse suna neman mafaka. A jiya Talata ne dai shugaban mai ci Umaro Sissoco Embalo, da babban...
    Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutum uku zuwa Majalisar Dattawa, domin tantance su a matsayin sabbin jakadan Najeriya. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Waɗanda aka zaɓa su haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawa da kuma Ayodele Oke. Bayan karanta takardar Tinubu, Akpabio ya ce, “Sunaye uku ne zuwa yanzu, tabbas sauran za su biyo baya.” Tun bayan ɗarewarsa kan mulki a 2023, Tinubu bai naɗa jakadu ba har yanzu. Mutane da dama sun daɗe suna ƙorafin kan jinkirin naɗa jakadun. Amma wasu na...
    Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar. Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take. ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Wannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa. A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane. Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar. A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar...
    Daga Salihu Tsibiri Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga  siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027. Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki. Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas. Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa...
    Hukumar tsaro ta DSS ta zargi dan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin kasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karbar Naira miliyan 50 daga kudin fansar fasinjojin. Ana zargin Tukur Mamu da karbar kudin ne daga jagoran ’yan bindigar da ake kira da “Shugaba”. Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Mamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000. Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida. Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai Ya tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu. Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya,...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ce ko sisi gwamnati ba ta biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 na sakandaren gwamnati ta Maga da ke jihar ba. Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, inda ya tabbatar da kubutar da ɗaliban da aka sace a farkon makon nan. Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Ya ce, “An karɓo ɗalibanmu da aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya ba jami’an tsaro umarni su gano inda yaran suke, kuma su kubutar da su. Muna tabbatar wa...
    Shugaban Iran ya sanar da cewa gwamnati na aiki don inganta juriya da ingancin tattalin arzikin kasar. Masoud Pezeshkian, Shugaban Iran, ya yi jawabi a taron Kasuwar Jarin Iran na shekara-shekara mai taken “Juriya, Kirkire-kirkire, Ci gaba,” yana mai jaddada gyare-gyaren manufofin tattalin arziki, kula da albarkatu, da kuma tallafawa masu zuba jari. Ya bayyana cewa gwamnati na aiki don rage cikas ga samar da kayayyaki da ciniki. Pezeshkian ya nuna muhimmancin yin tarurruka na wata-wata tare da masu zuba jari da masu samar da kayayyaki don nemo hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta. Ya kara da cewa, “Tanadin kashi 10% na iya adana ganga 800,000 zuwa 900,000 na mai a kowace rana.” Ya kuma nuna cewa samar da wutar...
    Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, yana mai jaddada muhimmancin Pakistan a yankin, ya ce haɗin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad a fannoni daban-daban yana taimakawa wajen kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce da sanyin safiyar Talata da ya isa Islamabad cewa Pakistan muhimmiyar ƙasa ce a yankin kuma tana da matsayi mai kyau wajen tasiri ga yanayin tsaro na yankin. A cewar Pars Today, ya ƙara da cewa a matsayinta na maƙwabciyar gabas ta Iran, Pakistan ma tana taka rawa a al’adu, kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana da zurfi kuma ta tarihi. Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci...
    Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
    Shugaban kungiyar Ansar Allah a Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya aika da sakon ta’aziyya ga Sakatare Janar na Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, kan shahadar babban  kwamandan dakarun kungiyar Haitham Ali al-Tabtabai da abokansa. Huthi ya jaddada cewa laifin da aka aikata a kansu, tare da hare-haren da ake kai wa Lebanon da Zirin Gaza, yana nuna irin girman kai da Isra’ila ke da shi ne. Sayyed al-Houthi ya kara da cewa shahid al-Tabtabai ya yi kokari matuka wajen cimma manyan-manyan nasarori, kuma ya ba da gudummawa ga hanyar gwagwarmaya don taimakon  gaskiya da wadanda aka zalunta, ya kara da cewa tasirin rawar da ya taka a cikin gwagwarmaya zai ci gaba da wanzuwa a cikin lamirin gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila...
    Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701. “Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701...
    Jami’an tsaro na kasar Siriya karkashin gwamnatin rikon kwarya ta HKI sun budewa masu zanga zangar lumana wuta a yankunan bakin ruwa na kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Talata ce, a garuruwan Tartus, Lazikiyya da lardin Lantakiya mutane suka fito zanga zanga ta lumana inda suke neman adlci ga Alawiyawa da sauran kananan addinin da mazhabobi a yankin. Har’ila yau da sakin wadanda gwamnati take tsare da su. Amma jawabin gwamnatin Jolani ga masu zanga-zangar shi ne aman wutan bindigogi da hayaki mai sa hawaye a kama masu zanga-zangar da dukan wasu daga cikinsu. Labarin ya kara da cewa matsalolin tsaro sun tarbarbare a yankin bakin ruwa na kasar Siriya sosai, tare...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu? NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci. An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi A cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira. Sabon harin, wanda ya faru da misalin...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa  yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan  Nuwamba a jihar. Shugaban  Hukumar Kula  Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya,  tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar. Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan. Ya ƙara da cewa rigakafin...
    An ceto ’yan matan nan 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar sakandaren Gwamnati ta GGCSS da ke yankin Maga da ke Jihar Kebbi. Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idiris a taron manema labarai a ranar Talata fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da an karɓo ɗalibban da aka sace a farkon makon nan. Ya ce “an karɓo ɗiyanmu ’yan makaranta waɗanda aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya baiwa jami’an tsaro umarni a tafi a gano inda yaran suke kuma a karɓo su muna tabbatar wa uwayen yara da al’ummar Kebbi yara sun dawo. “Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro musamman sojoji da ’yan sanda da Sibil difens da sauransu da suka...
    Babbar Mai Shari’ar ta kasa , Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta jaddada cewa alkalai suna da nauyin tabbatar da adalci cikin gaskiya da daidaito a lokacin da matsalolin tattalin arziki ke kara tsananta wa al’umma. Ta bayyana haka ne a Taron Alkalai na Shekara-shekara Karo na 26, wanda Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Koyar da Ayyukan Shari’a ta Kasa (NJI), a harabar Jami’ar da ke Kongo, Zariya. Mai Shari’a Kekere-Ekun, wadda Sakatare na NJI, Barista Abdulazeez Aluwo ya wakilta, ta ce dole ne kotuna su yi hukunci da ke la’akari da yanayin tattalin arziki da kuma hakkokin masu nema da wadanda ake binsu hukunci. Ta ce hakan ne kadai...
    Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies. Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci. An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba Dokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar. Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa. Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum. A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri. Malam Umar Namadi ya ƙara...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina. Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14, inda ta yi kunnen doki uku, sannan ta sha kashi shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Kafin wannan wasan, Kano Pillars ta yi wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba. Pillars ta zura kwallayenta ne ta hannun Rabiu Ali, wanda ya zura ta farko a...
    Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Isra’ila na yin kuskure idan ta na tunanin kashe-kashe da kisan gillar da ake wa mambobi da kwamandojinta zai kawo karshen kungiyar. Wannan na zuwa ne bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa babban kwamandan sojin kungiyar da wasu makusantansa a ranar Lahadi, a wani hari da ta kai a kudancin babban birnin Lebanon. Haitham Ali Al-tabataba’i  da aka fi sani da Abu Ali, ya yi shahada ne tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari  da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin beirut. Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun...
    Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu. A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko. Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama. Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka...
    ’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
    Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin. Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon gaba da maza biyu da mata shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Wani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu...
    Daga Musa kutama , kalaba Hasana Aminu matashiyar jaruma ce a Masana’antar Kannywood, wacce ta fito a finafina da dama ciki har da fim xin A Duniya da wasu fitattun finafunan Hausa. A zantawarta da Aminiya, Hasana Aminu wadda aka fi sani da suna Nabila ta ce, a halin yanzu tana tauna taura biyu ne a baka Ga yadda girar su ta kasan ce: Sunan Jarumar? Sunana Hasana Aminu, amma an fi sani na da suna Nabila a Masana’antar Kannywood da ke Kano Ta yaya kike gwama karatu da kuma kasuwanci da harkar fim? Eh, to farko ko da na shigo Masana’antar Kannywood sai na ga ai ashe ma ina da damar da zan iya yin karatu yayin da kuma...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 11, ciki har da wat mai juna biyu da ƙananan yara Jihar Kwara. Maharan sun kai farmaki tare da sace mutanen ne a yankin Eruku da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti da ke jihar. Ƙarin bayani na tafe…
    Gwamnonin jihohin  Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya. “Manufar taron ita ce samar da matsaya ɗaya wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke damun yankin, tare da tsara hanyar magance su,” in ji shi. Ya ƙara da cewa, za a yanke muhimman shawarwari a taron domin tabbatar da tsaron yankin. ’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu...
    Hukumar da take kula da harkokin watsa labaru a kasar Mali ta sanar da dakatar da ayyukan wasu kafafen watsa labarun kasar Faransa biyu a cikin kasar. Wadannan kafafen watsa labarun dai su ne LCI da TF1 saboda zarginu da watsa gubatattun labaru akan matsalar makamashi da ake fama da ita. TF1 dai tashar talabijin din Faransa ce mai zaman kanta da take watsa shirye-shiryenta a kasashe mabanbanta. Ita kuwa LCI ( La Chaine Info) tashar labarai ce wacce take a karkashin TF1. Hukumar dake kula da sanarwa a cikin kasar ta Mali ( HAC) ta rubuta wata wasika zuwa ga kafafen watsa labaru a ranar 13 ga watan Nuwamba wacce kuma a wannan makon mai karewa ne aka fito...
    A jiya Litinin ne dai mahukuntan kasar ta China su ka yi Allawadai da yadda kasar Japan din ta girke makamai masu linzami a wani tsibirinta da yake kusa da yankin Taiwan, tare da bayyana hakan a matsayin kokarin tayar da hargitsi a cikin yankin. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Máo Níng ta bayyana cewa: Daukar mataki irin wannan, wanda kuma ya zo bayan furucin Fira Ministar kasar ta Japan Sanae Takaichi,wani yanayi ne mai hatsarin gaske wanda yake da bukatuwa da kasashen yankin su kasance a cikin fadaka, haka nan kuma kungiyoyin kasa da kasa. Shi kuwa ministan tsaron kasar Japan ya bayyana cewa; Girke makamai masu linzami da kasarsa ta yi a tsibirin Yonagoni...
    ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
    Ana zargin wata amarya da yi wa angonta yankan rago kwana uku bayan ɗaurin aurensu a Jihar Katsina. Angon mai suna Abubakar Abdulkarim da aka fi sani da Dan Gaske, ana zargin ya rasa ransa bayan da amaryar ta yi amfani da wuƙa wajen halaka shi. Shaidu sun ce ta yi masa mummunan rauni a wuya wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Angon da amaryarsa suka daura aure ne a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2025, amma farin cikin aure ya rikide zuwa makoki a ranar Lahadi da rana lokacin da lamarin ya faru. Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta Wani ɗan uwansa mai suna Aminu...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan. A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan...
    Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa. Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta bazu zuwa gidajen da ke kusa. Duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, lamarin ya haifar da firgici inda mazauna yankin suka yi ta tserewa suka bar gidajensu yayin da tankar ke ci da wuta. Tankar mai ta yi hatsari a hanyar Lapai-Agaie Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro Mayaƙan Boko Haram sun fille kan mata 2 a Borno A wani...
    Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun.   Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye...
    Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadi jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun.   Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye...
    Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokacin kafa yansandan jihohi ya yi, har’ila yau dakuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar. Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da suka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo. Gwamnonin 6 sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika masu gadin dazuzzuka a shiyar kudu maso yammacin kasar don tabbatar da tsaronsu , sannan gwamnonin jihohin guda  shida ne zasu dauki nauyin kula da jami’an tsaron.  Labarin ya kara da cewa shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ne ya karanta jawabin bayan taron...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar. A  jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman abubuwan more rayuwa a karkara domin inganta harkokin tattalin arzikinsu. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Umar Namadi ya ce titin, wanda aka gina akan kudi Naira biliyan 1 da miliyan 690, na daga cikin manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi 48 da gwamnatinsa ta bayar a shekarar 2024. A cewarsa, titin zai hada al’ummomin karkara na Sada, Danakari, Unguwar Malam Kuda da Magina.   Ya...
    Gwamnatin Najeriya ta ce Amurka ta amince za ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu, wanda ya haɗa da samar da karin bayanan sirri, makamai da sauran kayan yaƙi, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a ƙasar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan Bayar da Bayanai da Tsara Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin. Atiku ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance Jarumin fina-finan Indiya Dharmendra ya rasu Wannan dai ya biyo bayan jerin tattaunawa da aka gudanar a Washington tsakanin manyan jami’an Najeriya da na Amurka, domin zurfafa dangantakar tsaro da ƙulla sabbin hanyoyin haɗin gwiwa. Tawagar Najeriya ƙarƙashin...
    Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon  na juyayin shahadar kwamanda haitham Ali Al-tabataba’i  da aka fi sani da Abu Ali wanda yayi shahada tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari  da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin berut na kasar labanon. Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun farko da aka kafata, kisan nasan ya kara nuna irin yadda isra’ila ke keta yarjejeniyar dakatar da tsagaita bude wuta da aka cimma, kuma kisan nasa zai kara karfafa jajircewa a turbar gwagwarmaya a yankunan labanon da falasdinu. Kungiyar hizbullah ta bayyana cewa babban kwamandan ya bi dan uwansa da yayi shahada...
    Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, da manyan makarantu—ciki har da Gwamnatin Tarayya da makarantu masu zaman kansu saboda matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a faɗin ƙasar kan. Sanarwa da Jalaludeen Usman Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, ya fitar ta ce, “Wannan shawara, duk da cewa tana da wahala, Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke ta ne bayan tattaunawa mai zurfi da kuma la’akari da matsalolin tsaro da suka shafi tsaron ɗalibai, malamai, da al’ummomin makarantu a faɗin jihar.” “Gwamnati ta san abin da wannan matsala ka iya haifarwa. Duk da haka, kare ’ya’yanmu ya kasance babban nauyin da ke kanmu. Muna sane da cewa lowane ɗalibi a Jihar...
    Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki. A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen kare ’yan Najeriya. A wani taro da ya yi da hukumomin tsaro a ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin cewa a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane. A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, daga yanzu rundunar ’yan sanda za ta mayar da jami’anta kan ayyukan tsaro na asali. Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan...
    Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya. “Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji...
    Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Indiya ta Bollywood, Dharmendra Deol da aka fi sani da Dharam Ji, ya mutu yau Litinin yana da shekaru 89 a duniya. Dharam ya riga mu gidan gaskiya ne kwanaki gabani cika shekaru 90 bayan fama da doguwar jinya mai alaƙa da numfashi kamar yadda kafofin labarai suka ruwaito. Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere A watan Nuwambar nan ne labaran ƙanzan kurege suka riƙa yaɗuwa cewa jarumin ya mutu a daidai lokacin da ake jinyar sa a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar ta Indiya. Bayanai sun ce tun dai cikin watan Oktoban da ya gabata,...
    Daga Bello Wakili Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawa da tawagarta ta yi da jami’an Amurka ta kara karfafa huldar tsaro tsakanin kasashen biyu tare da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa domin kara kare ‘yan Najeriya. Tawagar, karkashin jagorancin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ta  gana da manyan jami’an Majalisar Dokokin Amurka, Ofishin Bangaren Addini na Fadar White House, Ma’aikatar Harkokin Waje, Majalisar Tsaro ta Kasa da Ma’aikatar Yaki a birnin Washington DC A yayin tattaunawar, tawagar ta musanta zargin kisan kare dangi a Najeriya, tana mai jaddada cewa hare-haren da ake samu na shafar al’umma ne daga bangarori daban-daban na kabilu da addinai. Ta ce irin wannan kuskuren fassarar halin da ake ciki na haifar...
    Yundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin ’yan mata 14 da ƙungiyar ISWAP ta sace a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta kuɓuta, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran 13. A sanarwar da ya fitar dangane da irin ƙoƙarin da Jami’an tsaron ke yi na ceto sauran ‘yan matan 13 da ke hannun ‘yan ta’addan, kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce, shugaban gundumar Huyum ya bayar da rahoto a ranar Asabar 22 ga Nuwamba cewa waxanda ake zargin mayaƙan Ƙungiyar ISWAP ne suka sace ‘yan matan, yayin da suke aiki a wata gona a gundumar Mussa. Tawagar ’yan sanda, sojoji, Sibiliyan JTF, da mafarauta da ’yan banga nan da nan suka fara...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara ta sanya ranar 1 gawatan Disamba a matsayin wa’adin karshe na biyan kudin kujerar aikin Hajji na shekarar 2026, wanda ya kai sama da naira miliyan 7 da dubu 600. A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya jaddada cewa babu tabbaci yiwuwar karin wa’adi. Sanarwar ta ce  hukumar za ta tura kudaden Hajji ga Hukumar Aikin  Hajji ta Kasa (NAHCON)  domin cika wa’adin da Hukumar Hajjin Saudiyya ta gindaya. Haka kuma ta tabbatar da cewa fara aikin visa wato takardar izinin shiga kasar Saudiyya  zai kasance a watan Fabrairu 2026, kuma duk wani jinkiri na iya hana maniyyaci  samun damar zuwa aikin Hajjin na 2026....
    Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah az-Zahrah ( a.s) daya daga cikin masu tafiyar gaskiya akan tafarkin jagorar matan duniya, dan’uwa, mujahidin Haisam Ali Tabtabai’ ya yi shahada, tare da wasu manyan kwamandoji sanadiyyar harin ‘yan sahayoniya.” Dr.Ali Larijani ya kuma ce; Har yanzu Netanyahu yana ci gaba da tarbar aradu da ka, da hakan yake sake tabbatarwa da duniya cewa babu abinda ya kamata a yi sai kalubalantar wannan tsarin...
    A sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Lahadi ta ce; “A cikin dukkanin alfahari Hizbullah tana sanarwa da ‘yan gwgawarmaya da al’ummar Lebanon, shahadar babban kwamanda na jihadi Shahid Haisam Ali Tabtaba’i ( Sayyid Abu Ali) wanda ya yi shahada sanadiyyar harin wuce gona da iri na yaudara na Isra’ila a  yankin Harrik dake unguwar Dhahiya a kudancin Lebanon.” Sanarwar ta kuma kara da cewa; Shahidin ya hade da ‘yan’uwansa shahidai bayan tsawon lokaci na jihadi,gaskiya, kyakkyawar niyya da tsayin daka akan tafarkon gwgawarmaya da aikin da babu kakkautawa wajen fuskantar abokan gaba mhar zuwa lokaci na karshe na rayuwarsa.” Haka nan kuma sanarwar ta ci gaba da cewa; Shahidin yana cikin wadanda kafa harsashin gwgawarmaya saboda...
    Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya. “Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji...
    Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki. A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen kare ’yan Najeriya. A wani taro da ya yi da hukumomin tsaro a ranar Lahadi, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin cewa a janye ’yan sanda da ke gadin manyan mutane. A cewar mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, daga yanzu rundunar ’yan sanda za ta mayar da jami’anta kan ayyukan tsaro na asali. Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan...
    Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun sakandaren kwana a matsayin wani mataki na kariya ga ɗaliban makarantun. A cikin wata sanarwa da Mamman Mohammed, kakakin gwamnan, ya ce, wannan shawara ta biyo bayan taron tsaro tsakanin Gwamna Mai Mala Buni da shugabannin tsaro a jihar, inda suka yi nazari kan abubuwan da suka faru na tsaro a makarantu a wasu sassan ƙasar nan. Sanarwar da Babban Sakatare na ma’aikatar Ilimi na Jihar, Dakta Bukar, ya sanya wa hannu, ta umarci a rufe dukkan makarantun sakandare na kwana nan take har sai an samu ci gaba a lamarin. Gwamna Buni ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi wa shugabanni, jami’an tsaro, addu’ar ci-gaba da samun zaman lafiya...
    Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, da manyan makarantu—ciki har da makarantun Gwamnatin Tarayya da makarantu masu zaman kansu saboda matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a faɗin ƙasar kan. Sanarwa da Jalaludeen Usman Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, ya fitar ta ce, “Wannan shawara, duk da cewa tana da wahala, Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke ta ne bayan tattaunawa mai zurfi da kuma la’akari da matsalolin tsaro da suka shafi tsaron ɗalibai, malamai, da al’ummomin makarantu a faɗin jihar.” “Gwamnati ta san abin da wannan matsala ka iya haifarwa. Duk da haka, kare ’ya’yanmu ya kasance babban nauyin da ke kanmu. Muna sane da cewa lowane ɗalibi a...
    Kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a yammacin Asiya sun yi allawadai da hare-haren da HKI ta kai unguwar Dhahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiya Lahadi da yamma wanda ya kai ga shahadar mutane 5 da kuma raunata wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da babban kwamandan kungiyar Hizbullah Shahid Ali Tabatabai. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyoyi da kasashen da suka yi allawadai da hare-haren kamar haka. Akwain kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya wadanda suka hada da Hamas, Jihadul Islami, PFLP, kungiyar falasdinawa masu gwagwarmaya (PMM), Ansarullah mai gwagwarmaya. Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen JMI da kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki duk sun yi allawadai da hare-haren sun...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative.   Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da...
    Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad. Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare. Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici. Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi....
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce. Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi. Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba. Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a. Ta kuma ce ta...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi. An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN “‘Yan sanda biyar sun rasu, biyu sun jikkata, amma an yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar a ƙauyen Sabon Sara, Ƙaramar Hukumar Darazo, a jihar Bauchi.” Wakil, ya ƙara da cewa, “Ma’aikatanmu suna jajircewa kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin musayar wuta.” Ya bayyana ’yan...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar an ceto dukkanin mutanen da mahara suka sace a wata coci a yankin Eruku na Jihar Kwara. ’Yan bindigar sun sace masu ibadar ne a ranar Talata, lokacin da suka kai hari cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Oke Isegun a Eruku, wani gari da ke iyaka da Kogi a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji A cikin wani sako da Tinubu ya wallafa a X a ranar Lahadi, ya ce yana bibiyar yanayin tsaro a fadin kasar nan, kuma zai tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kare ’yan Najeriya. An yada bidiyon...
    Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno. Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan. Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a Kebbi Ya ce an sace ’yan natan ne yayin da suke aiki a gonakinsu da ke yankin Mussa. A cewarsa, ’yan matan guda 13 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20 sun tafi gona domin girbe amfanin gonarsu, sai maharan suka yi awon gaba da su. Tun da farko an mayar da mutanen Huyim zuwa Mussa saboda matsalar rashin tsaro a garuruwansu. Sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’yan matan da aka sace ta tsere kuma...
    Gwamnatin Jihar Kebbi ta umarci rufe dukkan makarantun sakandare na gwamnati da na kuɗi tare da dukkan manyan makarantun gaba da sakandare a faɗin jihar. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan Ilimi na Gaba da Sakandare Alhaji Issa Abubakar-Tunga da Kwamishinar Ilimi ta Firamare da Sakandare, Dakta Halima Bande, a Birnin Kebbi. Kwamishinonin sun bayyana cewa rufe makarantun gwamnati da na kuɗi a jiha ya zama dole sakamakon hare-haren da aka kai a wasu sassan jihar kwanan nan. Sun lissafa makarantun gaba da sakandare da abin ya shafa kamar haka: Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero da Kwalejin Kimiyyar...
    Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin  Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe. Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin kasuwanci da ake da shi a tsakanin kasashen da su ka ci gaba da masu tasowa wanda ya kamata a san yadda za a magance shi. Antonio Gutrres ya kuma ce: “Wani abu guda daya wanda zan iya bayar da tabbaci a kansa shi ne cewa ofishin babban magatakardar MDD zai yi duk abinda zai iya yi domin yin gyara a cikin rashin daidaito da...
    Gwamnatin Jihar Kebbi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun sakandire na gwamnati da na masu zaman kansu nan take. Haka kuma, gwamnatin ta rufe dukkan manyan makarantun gaba da sakandire a faɗin jihar, banda Kwalejin Nazarin Aikin Jinya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi. An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya  Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu, Alhaji Issa Abubakar-Tunga, tare da Kwamishiyar Ilimin Firamare da Sakandare, Dokta Halima Bande, suka fitar a Birnin Kebbi, ranar Lahadi. Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon barazanar hare-haren da ake samu a...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana adawarsa da duk wani mataki da zai iya kara tada hankali, musamman hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin Lebanon, yana mai jaddada “wajibcin janyewar sojojin mamaye.” Wannan ya zo ne a cikin sakon taya murna da Pezeshkian ya aika wa Shugaban Lebanon Joseph Aoun a ranar ‘Yanci, inda ya nuna godiyarsa ga al’ummar Lebanon da kuma fatansa na “lafiya, kwanciyar hankali, da wadata.” A cikin sakonsa, Pezeshkian ya bayyana cewa Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da Lebanon, jama’arta da gwamnatinta, kuma manufofinta marasa tabbas shine tallafawa kwanciyar hankali, wadata, da kuma zama tare tsakanin dukkan al’ummomin Lebanon. Ya kara da cewa Tehran na fatan “haɓaka haɗin gwiwa da dangantakar kasashen...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo. Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission Substation da ke Owerri, Jihar Imo, lamarin da ya janyo fargaba da tayar da hankali ga ma’aikatan da ke wurin. Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi A wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na ƙasa ya fitar, NUEE ta ce wannan hari na...
    161-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda wasu...
    Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita kissan kiyashi a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto magajin garin birnin NewYork musulmi na farko na cewa yana son shugaban Trump ya karkata kudaden da yake kashewa kan sojojin Amurka wadanda suke yake-yaken da masa da wani amfani ga mutanen kasar Amurka zuwa magance talaucin da Amurka suke fama da shi a cikin gida musamman masu kwana a waje a...
    A dai-dai lokacinda matsalolin tsaro suke kara tarbarbarewa a arewacin tarayyar Najeriya, kungiyar kiristoci ta kasa wato CAN ta bada sanarwan cewa yawan yaran da aka sace a ranar Jumma’an da ta gabat a makarantar St Mary a unguwar Papiri na karamar hukumar Agwara a jihar Naija ya kai 303. Daga cikin wadanda yan bingida suka sace har da malaman makarantar 12. Jaridar Premiumtimes ta Najeriya ta nakalto shugaban kungiyar Can a jihar Bulus Yohanna yana cewa sun tabbatar  da wannan labarin ne a binciken da suka gudanar a makarantar. Yohanna yace “Jimillar yan makaranta 303 ne aka sace, tare da malamansu 12, sannan wasu 88 da suka yi kokarin tserewa duk an kama su an tafi da su. Ya...
    Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gano wurin da ’yan bindiga suka tsugunar da ɗalibai mata 25 da suka sace daga makarantar kwana ta Maga da ke Jihar Kebbi. A wani taron manema labarai a Birnin Kebbi, Matawalle ya ce a halin yanzu an tsananta aikin leƙen asiri da tsare-tsare, tare da bayyana cewa ba da jimawa ba za a kuɓutar da ɗaliban cikin nasara, idan komai ya tafi yadda ake so. An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro Fiye da yara miliyan 400 na fama da talauci a duniya — UNICEF Ya nemi goyon bayan al’umma, yana mai cewa, “Haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci domin ganin an kammala wannan aiki lafiya lau,...
    Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Filato (PSUBEB) ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati a faɗin jihar sakamakon fargabar tsaro da ta taso a kwanakin nan. A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za a rufe ƙananan makarantun sakandare tun daga Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, yayin da makarantun firamare za a rufe su daga Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025. H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar Wannan mataki na zuwa ne bayan sace ɗalibai a wasu makarantu da ke jihohin Kebbi da Neja a ‘yan kwanakin da suka gabata, abin da ya tayar da hankalin iyaye da hukumomi....
    Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke addabar al’ummar Ƙaramar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana hakan bayan karɓar roƙon da jama’ar yankin suka miƙa ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar, Jamilu Ɗan Malam Mai Rice, kan yawaitar ambaliya a yankin. Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya A cewar Injiniya Bichi, “Mun karɓi kokenku hannu biyu. Matakin da shugabancin Jahun ya ɗauka ya yi dai-dai. Za mu tura ƙwararrun injiniyoyi su yi aikin da ya kamata domin daƙile ambaliyar, tare da inganta noman yankin...
    Gwamnatin Jihar Yobe, ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana a jihar domin kare ɗalibai, biyo bayan taɓarɓarewar rashin tsaro a wasu jihohin ƙasar nan. Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Asabar. Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Ya bayyana cewa an yanke wannan mataki ne bayan taro kan sha’anin tsaro da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tare da hukumomin tsaro, inda suka yi nazari kan barazanar da makarantu ke fuskanta a jihar. Sanarwar, wacce sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi, Dokta Bukar, ya sanya wa hannu, ta ce an rufe makarantun...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce matsalar tsaro a yankin Arewa na damunsa matuƙa saboda tana kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya. Ya bayyana haka ne a Jihar Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), wanda Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya wakilce shi. ’Yan sanda sun daƙile harin ’yan bindiga, sun ceto mutum 25 a Zamfara Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta gaji matsalolin tsaro masu yawan gaske, amma tana aiki tuƙuru don magance su. Ya yi gargaɗin cewa Najeriya ba za ta ci gaba ba idan al’ummarta suka ci gaba da fuskantar hare-hare, talauci, da tsoro. “Ba abin da ke damuna kamar...
    Rahotanni sun bayyana cewa an sanar da sunan brigadier janar Ali Jahanshashi a matsayin sabon kwamandan dakarun sojan kasar iran inda ya gaji brigadier janar Kiumars Haidari Bayanan da yayi jim kadan bayan sanar da nadin nasa a yau Asabar, Jahanshahi ya jaddada cewa dakarun sojin kasar a shirye suke su mayar da martani kan duk wata barazana ta hanyar amfani da kwarewarsu da makamai na zamani da kuma daukan darasi kan rikicin da ya faru abaya bayan nan musamman yakin kwanaki 12 da Israila ta kallafa mata. Haka zalika ya kara da cewa a halin yanzu sojoji sun bada fifiko ga kaidoji da dokoki guda 5 da jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah imam khamnai ya sanya, wanda suka...
    Daga Aliyu Lawal  Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar sakamakon sace dalibai da aka yi a Makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Karamar Hukumar Agwara. Gwamna Mohammed Umar Bago ne ya sanar da hakan a Minna bayan wata tattaunawar tsaro gaggawar  ta da aka gudanar da shugabannin hukumomin tsaro, malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki. Ya ce matakin ya zama wajibi domin kare rayukan dalibai yayin da ake kara kokarin ceto yaran da aka sace. Gwamna Bago ya jaddada cewa yanzu lokaci ne na daukar mataki a maimakon zargin juna, inda ya bayar da umarnin cewa a rufe...
    Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro. Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja Mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba. Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar...
    Daga Isma’il Adamu  Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati,  da na masu zaman kansu a fadin jihar biyo bayan kalubalen tsaro da ya addabi makarantun kasar nan. Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu hare-haren sace ɗaliban makarantu da suka faru a jihohin Kebbi da Neja kwanan nan. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare, Sani Danjuma, ya sanyawa hannu, ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin nuna jajircewar gwamnati wajen kare ɗalibai, malamai da ma’aikatan makarantu. Sanarwar ta ce duk da cewa rufe makarantun na iya kawo cikas ga iyaye da ɗalibai, tsaro ya fi komai muhimmanci yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro a...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya fara mayar da rarar kuɗin ga maniyyata, sakamakon rage kudin kujerun Hajjin 2026 da Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya rabawa manema labarai, ya ce Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa za a mayar da rarar kuɗin ne ga maniyyatan da suka kammala biyan kudadensu a fadin jihar kafin a sanar da rage kudaden. Ahmed Labbo ya ce NAHCON ta bayyana sabon farashin cewa yankin Arewa zai biya sama da Naira Miliyan 7.6, yayin da waɗanda za su tashi daga yankin Kudu za su biya sama...
    Kwamandan sojan kasa na Rudnunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgerdiya Janar Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin kasar a shirye suke su mayar da martani akan duk wata barazana daga abokan gaba saboda suna da zaratan mayaka da kuma sabbin makamai.” Har ila yau Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin za kuma su yi amfani da kwarewar da tsofaffin sojoji suke da ita, haka nan kuwa darussan da su ka koya daga kallafaffen  yakin kwanaki 12 da HKI.  Janar Jahanshahi ya kuma ce; A wannan lokacin kwarewar da sojojin kasa na Iran suke da su, ta kai koli saboda wararrun masana da kuma amfani da fannoni mabanbanta na ilimomi, musamman kirkirarriyar Fasaha.” A dalilin hakan, sojojin suna cikin Shirin mayar wa...
    Fira Ministan kasar Madagascar Herintsalama Rajaonarivelo ya gabatar da jadawalin ayyukan siyasa a gaban  majalisar kasar, da a ciki ya kunshi yadda zaman gwamnatin rikon kwarya zai kasance da yadda zai kai ga yin manyan zabukan kasar a cikin shekara daya da rabi. Fira ministan kasar ta Madagascar ya kuma ce; A karshen watan farko  na gwamantin rikon kwarya ne za a bude ttataunawa a fadin kasar, wanda kuma zai ci gaba har tsawon watanni shida. Daga nan kuma za a bude tataunawa akan madogarar shari’a da yi wa hukumar zaben kasar kwaskwarima. Bugu da kari, fira ministan ya ce, gwamantin rikon kwaryar za ta so shirya zabuka bayan watanni 14 zuwa 20 daga hawanta karagar Mulki. Dangane da matsalolin...
    Gwamnatocin jihohin Katsina da Taraba sun ba da umarnin rufe makarantu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka sace daruruwan ɗalibai a makarantu a cikin mako guda a jihohin Kebbi da Neja. Gwamnatin Jihar Taraba ta rufe makarantun kwana a fadin jihar, inda ta ba da umarnin a koma tsarin jeka-ka-dawo sakamakon tabarbarewar tsaro. Gwamnan Agbu Kefas, ya umarci duk makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dalibai su daina kwana a makarantu saboda fargabar tsaro a faɗin ƙasar. Sanarwar da kwamishinar ilimi ta jihar, Augustina Godwin, ya fitar ta ce garkuwa da ɗalibai a Kebbi da Neja ta sanya daliban makarantun kwana zama cikin hadari. Don haka gwamnati ta umarci komawa tsarin jeka-ka-dawo har sai tsaro ya inganta....
    Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya  saboda matsalolin tsaro. A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk wani yunkurin hari, Ministan Ilimi ya amince a rufe makarantun nan dltaje. Ga jerin makarantu da abin ya shafa: Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Minjibir, Jihar Kano Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ganduje, Jihar Kano Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Zariya, Jihar Kaduna Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kafanchan, Jihar Kaduna Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bakori, da wacce ke Bwari, Abuja. Kwalejin Fasaha...
    Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar domin kwashe ’ya’yansu bayan harin, amma ba ba su yaran ba. A baya  Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kutsa cikin makarantar da daddare a ranar Juma’a, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makarantar. Shugaban Cocin Katolika ta Kontagora, Mai Girma Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya sanar ta hannun mai taimaka masa, Daniel Atori, cewa an yi garkuwa da ɗalibai 303, malamai...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
    Shugaban kasar Ukrain Volodymyr Zelensky ya fito fili ya bayyana cewa bai amince da sabon shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na kawo karshen yaki a kasarsa. Ya kuma bayyana cewa kasar Ukraine tana cikin mafi munin hali a tarihin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka yana takurawa kasarsa ta amince da al-amura guda 28 da ya gabatar wanda a fadinsa zai kawo karshen yakin shekari kimani 3 wanda kasarsa take fafatawa da kasar Rasha. Labarin ya kara da cewa daga cikin al-amuran da shugaban ya gabatar a wannan shirin kawo karshen yaki a Ukraine sun hada da amincewa da zaben...
    Yan wasan kasar Iran sun kammala gasar wasannin sada zumunci na kasashen musulmi wanda aka kammala a birnin Riyad na kasar Saudiya tare da lambobin yabo har 81. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan ya nuna cewa kasar Iran na daga cikin kasashen musulmi wadanda suke da kwarewa a wasannin motsa jiki daban daban. Labarin ya kara da cewa an gudanar da wasannin ne daga ranar 6 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan. Tare da fara wasu wasannin daga ranar 3 ga watan. Kasar Saudiya wacce ta dauki bakwancin wadan nan wasannin motsa jiki ta sami nasarar tattara yan wasannin motsa jiki na kasashen musulmi a duniya a cikin kwanaki kima 20 da suka...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse. Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci. Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa  mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani. “Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne...
    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro. Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa. Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure. Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis...
    Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi  Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba. Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba. Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan...
    Hukumar DSS ta mayar d Shugaban ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato. Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke masa na ɗaurin rai da rai kan laifukan ta’addanci. Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi  Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa A ranar Alhamis ne, Alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, James Omotosho, ya ce DSS za su kai Kanu kowace cibiyar gyaran hali da ke Najeriya. Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya tabbatar da mayar da shi Sakkwato aranar Juma’a. Ya ce: “DSS ta ɗauke Mazi Nnamdi Kanu daga gidan yari na Abuja zuwa  Sakkwato, sun nesanta shi da...
    Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare. Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta “An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris. Ya...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa. Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure. Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis...