Birtaniya ta dage takunkumin da ta kakaba wa wasu manyan jami’an Zimbabwe
Published: 28th, May 2025 GMT
Gwamnatin Birtaniya ta sanar da dage takunkumin da ta kakaba wa wasu manyan jami’an gwamnatin Zimbabwe.
Birtaniya ta ce ta yi hakan ne domin kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniyar ta bayyana cewa za ta dage takunkumin da ke kan mutum hudu da kuma kamfanin kera makamai mallakar gwamnati a Zimbabwe.
Wannan matakin ya zo watanni bayan Tarayyar Turai ita ma ta sassauta nata takunkumin kan Zimbabwe.
Birtaniya ta saka takunkumin ne a lokacin saboda damuwa da abinda ta kira take hakkin dan Adam da aka rika samu a kasar ta Zimbabwe.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Birtaniya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
Ta ce: “Kotu ba ta bayar da umarni ba? Ba ku da ikon karɓe fasfona.”
Ba a bayyana wata hujja ko dalili a hukumance ba kan dalilin karɓe fasfo ɗin nata ba, lamarin da ya sa wasu suka zargi cewa ana shirya mata maƙarƙashiya irin ta siyasa.
An hangi mijinta, Cif Uduaghan, yana kiran waya cikin sauri yayin da lamarin ya ɗauki lokaci.
Bayan ‘yan mintuna, jami’an sun mayar mata da fasfo ɗin ba tare da wani bayani ba.
An bar ta ta shiga jirgin kafin ya tashi.
Wasu daga cikin fasinjojin da suka shaida lamarin sun bayyana abin a matsayin abin kunya, inda suke kallon lamarin a matsayin amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba.
Har yanzu, hukumar shige da fice ta ƙasa da ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ba su ce komai ba game da lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp