Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu.

Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar.

Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya 

Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar.

Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin bayan cece-kucen da hakan ya haifar a faɗin ƙasar.

Ƙudurorin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke nazari a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.

Aminiya ta ruwaito cewa, majalisar ta janye ƙudirin ne bayan gwamnatocin jihohin sun bayyana adawarsu kan matakin da ke neman tuɓe musu rigar alfarmar da ke bai wa gwamnoni da mataimakansu da kuma mataimakin shugaban ƙasa kariya daga fuskantar tuhuma kan laifuka.

A ranar Larabar da ta gabata ce ƙudirin ya samu karatu na biyu a zauren majalisar, ƙarkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai

এছাড়াও পড়ুন:

Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Gwamnatin Sudan da ke da goyon bayan sojoji ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana bayyana ƙasar a matsayin mai katsalandan, a cewar Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim.

A cikin jawabin da aka watsa a talabijin ranar Talata, Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat ɗinta a ƙasar Gulf ɗin.

Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi Inter Milan ta kori Barcelona daga Gasar Zakarun Turai

Ya zargi UAE da take hurumin Sudan ta hanyar “ƙawarta”, wato Rundunar RSF, wacce ke yaƙi da sojojin Sudan tun watan Afrilu 2023.

“Dukkan duniya ta shaida, fiye da shekaru biyu, laifin kai hari kan hurumin Sudan, cikakken yankinta da kuma tsaron ‘yan ƙasarta da UAE ke yi ta hanyar ƙawarta ta cikin gida, wato ƙungiyar ‘yan ta’adda ta RSF,” in ji ministan.

Gwamnatin Sudan ta sha zargin UAE da samar wa RSF makamai — zarge-zargen da Abu Dhabi ya musanta.

Matakin da gwamnatin Sudan ta ɗauka ya biyo bayan harin jirage marasa matuƙa a Port Sudan — wanda yanzu ya zama babban birnin ƙasar na wucin gadi — wanda aka kai har sau uku a jere.

Ibrahim ya ce UAE ta ƙara tsananta shiga cikin rikicin ta hanyar samar wa RSF “makamai masu ci gaba na zamani” bayan nasarorin da sojojin Sudan suka samu a filin daga, inda suka sake karɓe iko da babban birnin Khartoum a watan Maris.

Ya ƙara da cewa Sudan za ta “mayar da martani ga wannan hari ta kowace hanya da ta dace don kare hurumin ƙasar” da kuma “kare fararen hula.”

Yaƙin da ya yi sanadin mace-mace

Yaƙin da ke gudana a Sudan ya kashe dubban mutane, ya raba mutane miliyan 13 da muhallansu, kuma ya haifar da babbar matsalar gudun hijira da yunwa a duniya.

Rikicin ya raba ƙasar gida biyu, inda sojojin ke iko da arewa, gabas da tsakiyar ƙasar, yayin da RSF ke mamaye mafi yawan yankin Darfur na yamma da wasu sassan kudu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Gudanar Da Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasara A Yakin Duniya Na Biyu
  • Ficewar ’yan majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren majalisar Wakilai
  • A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci – Ganduje
  • Kakakin Gwamnatin Iran Ta Yi Suka Kan Masu Son Canja Sunan Tekun Fasha Saboda Jahilcin Tarihin Iran
  • Ma’aikatar Yaɗa Labarai Ta Fara Bitar Ayyuka Na Tsakiyar Wa’adi
  • An Tabbatar Da Ficewar Sanata Sumaila Daga NNPP Zuwa APC A Majalisa
  • APC: Na Bar PDP Ne Domin Ci Gaba Da Amfana Da Ribar Ofishi Na – Kakakin Majalisar Edo
  • Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
  • Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus
  • Xi Da Shugaban Majalisar Turai Da Shugabar Kwamitin EU Sun Tayawa Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Hulda