Amurka sake kai sabon hari kan kasar Yemen
Published: 5th, May 2025 GMT
Amurka na kara kai hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na kasar Yemen.
Babban birnin kasar, Sanaa, shi ne Amurka ta kai wa hari a safiyar yau Litinin.
Wasu hare-hare ta sama da Amurka ta kai a yankunan Bani Matar, Bani Hushaysh da Bani Al-Harith a birnin Sanaa.
Hakazalika, harin da jiragen yakin Amurka suka kai kan wata kasuwa da ke gundumar Shu’ab ta birnin San’a ya lalata shaguna da dama.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Yemen, wasu ‘yan kasar 14 ne suka jikkata sakamakon harin da Amurka ta kai a yankin kasuwanci.
Garin Saada da ke arewa maso yammacin kasar, shi ma ya fuskanci hare-hare uku na Amurka.
Bugu da kari, wasu hare-hare ta sama na Amurka sun auna yankuna biyu na yankunan Maarib da al-Jawf na kasar Yemen.
Kakakin Kwamitin Tsaron Amurka James Hewitt, ya ce sojojin Amurka sun kai hare-hare sama da 1,000 a kan Yeman kuma za su ci gaba da kai hare-hare tare da hada kai da Isra’ila.
Hare-haren dai ya biyo bayan nasarar harba makami mai linzami da Yeman ta kai kan yankunan falasdinawa da aka mamaye, wanda ya afkawa filin jirgin sama na Ben Gurion da ke Tel Aviv, lamarin da ya janyo tsaikon zirga-zirgar jiragen sama.
Mutane 8 ne suka jikkata a cewar ma’aikatan jinya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hare hare ta
এছাড়াও পড়ুন:
Yemen Ta Kai Wa HKI Hari Da Makami Mai Linzami Na “Falasdinu 2”
Sojojin kasar ta Yemen sun sanar da kai wa yankin Yafa hari da makami mai linzami da ya fi sauti sauri mai suna ” Falasdinu 2″, tare da tabbatar da cewa, ya fada inda aka harba shi.
A yau Asabar ne dai sojojin na Yemen su ka kai wa HKI harin da makami mai linzami mai tsananin sauri bisa abinda su ka kira da cewa; Mayar da martani ne akan ci gaba da yakin da yakin da ‘yan sahayoniya suke ci gaba da kai wa Gaza, da kuma jefa yankin cikin yunwa.
Kakakin sojan kasar Yemen, janar Yahya Sari, ya bayyana cewa; Makami mai linzamin da aka yi amfani da shi sunashi; “Falasdinu 2” kuma ya isa inda aka harba shi.
Janar Yahya Sari ya kuma ce: Dukkanin al’ummar musulmi ne suke da alhakin yin shiru akan abinda yake faruwa a Gaza, da kuma kin taimaka musu, sannan kuma ya ce: Ko ba dade-ko bajima, samamakon yin shiru akan wuce gona da irin ‘yan sahayoniya zai isa cikin sauran kasashe.”
Janar Sari ya kuma ce; Gaza, tana kare dukkanin al’umma ne a wannan lokacin, domin taimaka mata shi ne ya fi dacewa da a tsumayi lokacin da sharri zai isa gidan kowa.”
Da safiyar yau Asabar ne dai jiniyar gargadi ta kada a yankuna da yawa na HKI da su ka hada yankin Kudus, Tel Aviv da kuma ” “Dead Sea” bayan da aka harbo makami mai linzami daga kasar ta Yemen.
Makamin na dazu dai ne karo na uku da sojojin Yemen su ka harba a cikin sa’o’i 24.