An labarto cewa harin ya wakana ne da safiyar ranar Lahadi kuma ‘yan bindigan sun yi awun gaba da shanu da sauran dabbobin al’umman yankin a yayin farmaƙin.

 

Kazalika, wakilinmu ya gano cewa baya ga ‘yan bijilante da suka rasa rayukansu akwai wasu fararen hula mazauna ƙauyen Sabuwar Sara su ma sun gamu da ajalinsu yayin da suke ƙoƙarin gudun neman tsira bisa harbe-harben ‘yan bindigan.

Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa su ma ɓangaren ‘yan fashin dajin sun rasa mutanensu da dama da ake hasashen sun ma fi ‘yan Bangan mutuwa.

 

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta bayyana haƙiƙanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a ɓangaren ‘yan Banga da ‘yan fashin ba.

 

A sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin, kakakin rundunar , CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 05:40 a ranar 4 ga watan Mayun 2025, inda aka kai rahoton faruwar hakan ga shalkwatar ‘yansanda da ke Alkaleri da ƙarfe 09:40.

 

“Haɗakar ƙwararrun mafarauta daga gundumomin Duguri da Gwana a lokacin da suke aikinsu na sintiri a dajin Mansur, da Dajin Mada, iyaka da jihar Bauchi da jihar Filato, kwatsam sai suka ci karo da tawagar ‘yan fashin daji inda suka musu kwantan ɓauna domin farmaƙarsu,” Wakil ya shaida.

 

Ya ƙara da cewa bisa musayar wuta da aka yi a tsakaninsu, dukkanin ɓangaren sun raunata daga su kansu ‘yan Bijilante da kuma maharan.

 

Kakakin ya ce an tura jami’an ‘yansanda wurin da abun ya faru inda suka kwaso gawarwakin da aka kashe.

 

Binciken farko-farko na ‘yansansa shi ma ya tabbatar da cewa waɗanda suka rasu an samesu ne a dukkanin ɓangarorin biyu har ma wasu fararen hula daga ƙauyen Sabuwar Sara lamarin ya shafa a lokacin da suke neman tsira da rayukansu.

 

Sai dai, rundunar ta ce tunin aka ƙaddamar da bincike domin ganin an kamo ‘yan fashin dajin domin tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a.

 

Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi tur da harin tare da tura jami’ai domin su gana da al’ummar kauyen Mansur domin neman hanyoyin da za a inganta tsaro.

 

Ya jajanta wa iyalan wadanda aka kashe inda ya ba su tabbacin nema musu adalci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina
  • An Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 12, An Kwato Makamai A Katsina
  • EFCC Ta Kama Tsohon Kakakin Majalisar Filato Da Wasu ‘Yan Majalisa 14 Bisa Zargin Almundahana
  • Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato
  • Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyen Kebbi, Sun Kashe Mutane Da Dama
  • Ambaliyar Mokwa – Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin Neja
  • An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana
  • Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump
  • Sabon Shirin Gwamnatin Katsina: Za A Fara Sauya Tunanin Tubabbun ‘Yan Bindiga