Wasu ’yan bindiga da ake fargabar mayaƙan Lakurawa ne sun kashe wasu ’yan bijilanti da ke aikin sintiri a Jihar Sakkwato.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan musayar wuta da mayaƙan suka yi da ’yan sintiri a Ƙaramar Hukumar Tangaza a jihar ta Sakkwato.
Ya kamata a zuba jari a harkar noman rani — Zulum Wa zai cire wa Real Madrid kitse a wuta?
Bayanai sun ce kawo yanzu akwai ragowar gawawwakin ’yan bijilantin da ke hannun Lakurawan a dajin da suka yi sansani.
Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa rundunar soji na ƙoƙarin ƙwato gawawwakin a dajin Binji da Raka.
Shaidu sun ce tun da farko lamarin ya faru ne yayin da ’yan sintirin suka yi ƙoƙarin hana ’yan bindigar shiga ƙauyen Magonho domin kai hari.
Wannan ce ta sanya aka soma musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya kai ga salwantar rayukan ’yan bijilantin.
Rahotanni na cewa ’yan bindigar aƙalla 40 haye a kan babura 20 ne suka kai harin da nufin satar dabbobi kafin a ci ƙarfinsu su tsre.
“Sun kashe mana mutane 11 sun kwashi wasu gawar namu sun tafi da su domin wulaƙanci, zuwa yanzu ba za a ce ga yawan mutanen da suka tafi da su.”
Sai dai sojojin da suka yi sansani a yankin sun kawo ɗauki, inda suka yi nasarar ƙwato wasu dabbobni hannunsu.
Kazalika, daga bisani ’yan bindigar sun koma ƙauyen Magonho inda suka tarwatsa turakun sadarwa na kamfanin MTN.
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Rufa’i Ahmad, amma lamarin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan sintiri
Lakurawa
Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu ma’aurata da wasu mutane biyar bisa zarginsu da gudanar da ɗaurin aure ba tare da izinin iyayensu ba ko kuma bin tsarin addinin Musulunci a unguwar Nasarawa da ke cikin birnin Kano. Wadanda ake zargin sun hada da ango mai suna Aminu mai
shekaru 23 da amaryarsa Sadiya mai shekaru 22. Sauran
wadanda aka kama su ne Umar mai shekaru 24 wanda ya kasance wakilin ango; Abubakar, mai shekaru 23, wanda ya kasance waliyyin amarya; Usaina, mai shekaru 21; da kuma wasu ‘yan mata guda biyu wadanda suka kasance shaidu a yayin ɗaurin auren. Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya Rahotanni sun bayyana cewa, an ɗaura auren ne akan sadaki Naira 10,000, ba tare da amincewar iyayen ma’auratan ba. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin babban kwamandan hukumar ta Hisbah, Dr. Mujaheeddeen Aminuddeen, ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan korafe-korafen da ‘yan unguwar suka kai wa hukumar. Ya bayyana cewa, matakin da wadanda ake zargin suka ɗauka ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci da kuma dokokin aure na jihar, yana mai jaddada cewa, hukumar ta Hisbah ba za ta amince da duk wani abu da ya saɓawa tsarin addini da na shari’a a jihar Kano ba. Dr. Aminudeen ya kara da cewa, a halin yanzu wadanda aka kama suna hannun Hisbah domin ci gaba da bincike. ShareTweetSendShare MASU ALAKA

Ra'ayi Riga Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang October 13, 2025

Labarai Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista October 13, 2025

Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025