Bayanai daga Amurka na cewa Hannayen jari na kafofin watsa labaru da kamfanonin shirya fina-finai da harkokin nishadi na Amurka sun fadi kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, yana shirin kakaba harajin kwastam da kashi 100 bisa 100 a kan fina-finan da ake shiryawa a ketare.

Hannayen jarin kamfanonin fina-finai irin su Netflix Inc.

da Warner Bros. Discovery Inc. sun fadi da kusan kashi 3 cikin dari, inda na Paramount Global da Walt Disney Co. kuma suka fadi da kusan kashi 2 cikin dari yayin da aka bude kasuwa.

A wani sakon da ya wallafa kan shafinsa na manhajar True Social, shugaban na Amurka ya ce yana umurtar ma’aikatar kasuwanci da wakilinsa na cinikayya da su “yi maza-maza su fara aikin kakaba” harajin a kan fina-finan kasashen waje, inda ya kara da cewa, “Muna son kara ganin fina-finan da ake yi a Amurka”.

Shugaban ya kuma sanya fina-finan kasashen waje a cikin jerin abubuwan dake kawo barazana ga tsaron kasa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Pakistan Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Mai Cin Tazarar Kilo Mita Fiye Da 400

Sojojin kasar Pakistan sun sanar da yin nasarar gwajin makamai mai linzami da ake harbawa daga kasa, wanda yake cin Zangon kilo mita 450.

Sanarwar sojojin kasar ta Pakistan ya kunshi cewa; Sun yi gwajin ne dai domin tabbatar da zama cikin shiri na sojoji, da kuma tabbatar da ingancin aikin makamin.

Gwajin makamin na sojojin Pakistan ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a tsakaninta da kasar Indiya, bayan wani harin ta’addanci da aka kai a yankin Kashmir.

A ranar 22 ga watan Afrilu ne dai aka kai wani hari akan masu yawon bude ido a yankin na Kashmir wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 26. Da akwai fargabar cewar kasashen biyu za su tsunduma cikin wani sabon yaki,bayan da Indiya ta zargi Pakistan da cewa tana da hannun a wancan harin.

Pakistan dai ta kore cewa tana da hannu, tare da yin kira ga Indiya da ta kaucewa tsokana, domin za ta mayar da martanin da ya dace gwargwadon harin da za ta kai mata.

Mahukuntan kasar Pakistan sun gargadi Indiya akan cewa, su kwana da sanin cewa; Islamabad tana da makaman Nukiliya.

A yau Asabar an yi musayar wuta a tsakanin sojojin kasashen biyu a tsawon yankin da ya raba su a yankin Kashmir.

A jiya Juma’a mahukunta a yakin Kashmir sun yi kira ga mazauna yankin da su tanadi  abincin da zai  ishe su na tsawon watanni biyu,saboda tsoron yiyuwar barkewar yaki a tsakanin kasashen biyu masu karfin Nukiliya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sharhin bayan Labarai: Ci Gaban Harkokin Kasuwanci Tsakanin Iran Da Kasashen Waje Duk Tare Da Takunkuman Kasashen Yamma
  • CMG Ya Kaddamar Da Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Talabijin Na Kasar Sin Masu Inganci A Rasha
  • Kada ku karaya da shigo da abinci daga ƙasar waje — IAR
  • Gwamnan California: California Za Ta Ci Gaba Da Bude Kofa Ga Sin Domin Gudanar Da Kasuwanci
  • Trump Na Shan Suka Kan Wallafa Hotonsa Na AI Sanye Da Kayan Fafaroma
  • Nijeriya Ta Yi Asarar Naira Biliyan 118 Sakamakon Barnatar Da Iskar Gas A Watanni 2
  • Kasar Yemen Ta Kakaba Takunkumi Kan Amurka A harkokin Fitar Da Man Fetur Din Kasarta
  • Pakistan Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Mai Cin Tazarar Kilo Mita Fiye Da 400
  • Dakataccen Gwamnan Ribas Ya Dawo Daga Hutun Makonni Biyu A Kasar Waje