Tarayyar Turai: Muna Goyon Bayan Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diplomasiyya
Published: 5th, May 2025 GMT
Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya.
Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun Nukiliyar Iran da kuma rage rikice-rikice a cikin wannan yankin.
Haka nan kuma Kallas ta jaddada abinda a baya tarayyar turai din ta rika riyawa da ba shi da tushe na cewa, Iran tana bai wa Rasha taimakon soja tana mai cewa: ” Na kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da bai wa Rasha taimakon soja.”
Iran dai ta sha yin watsi da wannan irin zargin na cewa tana bai wa kasr Rasha makamai.
Matsayar tarayyar turai din dai ta zo ne bayan yin zango na uku na tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman wacce aka fara tun a karshen watan Afrilu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tarayyar turai
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta watsi da zargin Isra’ila da Amurka cewa ta na da hannu a harin ramuwar gayya na Yemen
Iran ta yi kakkausar suka da kakkausar murya kan zargin Amurka da da na Isra’ila suka cewa ta na da hannu a hare-haren ramuwar gayya na kasar Yemen.
Iran ta ce zarge zagren basu da tushe balle makama.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya fada a yammacin jiya Lahadi cewa, matakin da kasar Yemen ta dauka na goyon bayan al’ummar Falasdinu, wani mataki ne mai cin gashin kansa, wanda aka dauka a matsayin goyan bayan Palasdinawa.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada cewa, sojojin Amurka ne suka shiga yakin domin tallafawa kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawa ke ci gaba da yi a zirin Gaza.
Don haka Araghchi ya soki Amurka da aikata laifukan yaki ta hanyar kai hare-hare kan ababen more rayuwa da wuraren fararen hula a garuruwan Yemen.
Araghchi ya kira hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Yemen a matsayin cin zarafi ga kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da muhimman ka’idojin dokokin kasa da kasa.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ci gaba da cewa zargin da ake yi na baya-bayan nan wata dabara ce ta karkatar da hankali daga laifukan da gwamnatin sahyoniyawan ta ke aikatawa a Falastinu, da boye irin gazawar da Isra’ila da kawayenta suka yi a cikin dabarunta, da kuma tabbatar da ci gaba da tada zaune tsaye a yankin.