’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansa
Published: 5th, May 2025 GMT
’Yan bindiga sun kashe wata mata da suka sace tare da mijinta Yakubu Dada watanni bakwai da suka gabata a yankin Kontagora da ke Jihar Neja.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan sun halaka matar mai suna Lami bayan karɓar Naira miliyan 10 kuɗin fansa.
’Yan fashi sun kashe matashi a Kano Kwankwaso: Abba ya mayar wa Baffa Bichi martaniKazalika, ’yan bindigar sun kuma nemi ƙarin Naira miliyan 20 da baburan Bajaj huɗu, tare da yin barazanar kashe mijinta muddin aka gaza kai musu abubuwan da suka buƙata.
Aminiya ta ruwaito cewa, tun a ranar 31 ga watan Oktoba na 2024 ne Yakubu Dada da mai ɗakinsa suka faɗa tarkon masu garkuwa yayin da suke kan hanyar zuwa Kontagora.
Da take zantawa da wakilinmu, uwargidan magidancin mai suna Maimuna, ta ce sun cefanar da kusan duk abin da suka mallaka ciki har da gidaje, motoci, gadaje, akwatin talabijin domin tara kuɗin fansar naira miliyan 10 da suka biya a watan Nuwamban bara.
Ta ce wani ƙanin mijinsu ne ya kai wa masu garkuwar kuɗin fansar a wani daji a Jihar Kebbi, amma daga bisani suka nemi ƙarin naira miliyan 60 sannan suka sassauta zuwa naira miliyan 20 da har kawo yanzu sun gaza biya.
Maimuna wadda ta ce masu garkuwa sun kashe abokiyar zamanta a ranar Lahadin da ta gabata, ta buƙaci gwamnatin jihar Neja da hukumomin tsaro da su shiga lamarin domin ceto mijin nasu.
Wani makwabci, Idris Mohammed, ya ce an yi kiran neman tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa a yayin sallar Juma’ar da ta gabata tun kafin labarin mutuwar Lami.
Aminiya ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, sai dai ya yi alƙawarin zai bibiyi lamarin gabanin cewa komai a kai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga garkuwa da mutane Jihar Neja matar aure
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato
Wasu ’yan bindiga da ake fargabar mayaƙan Lakurawa ne sun kashe wasu ’yan bijilanti da ke aikin sintiri a Jihar Sakkwato.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan musayar wuta da mayaƙan suka yi da ’yan sintiri a Ƙaramar Hukumar Tangaza a jihar ta Sakkwato.
Ya kamata a zuba jari a harkar noman rani — Zulum Wa zai cire wa Real Madrid kitse a wuta?Bayanai sun ce kawo yanzu akwai ragowar gawawwakin ’yan bijilantin da ke hannun Lakurawan a dajin da suka yi sansani.
Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa rundunar soji na ƙoƙarin ƙwato gawawwakin a dajin Binji da Raka.
Shaidu sun ce tun da farko lamarin ya faru ne yayin da ’yan sintirin suka yi ƙoƙarin hana ’yan bindigar shiga ƙauyen Magonho domin kai hari.
Wannan ce ta sanya aka soma musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya kai ga salwantar rayukan ’yan bijilantin.
Rahotanni na cewa ’yan bindigar aƙalla 40 haye a kan babura 20 ne suka kai harin da nufin satar dabbobi kafin a ci ƙarfinsu su tsre.
“Sun kashe mana mutane 11 sun kwashi wasu gawar namu sun tafi da su domin wulaƙanci, zuwa yanzu ba za a ce ga yawan mutanen da suka tafi da su.”
Sai dai sojojin da suka yi sansani a yankin sun kawo ɗauki, inda suka yi nasarar ƙwato wasu dabbobni hannunsu.
Kazalika, daga bisani ’yan bindigar sun koma ƙauyen Magonho inda suka tarwatsa turakun sadarwa na kamfanin MTN.
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Rufa’i Ahmad, amma lamarin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton