Aminiya:
2025-05-06@12:46:17 GMT

NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya?

Published: 6th, May 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma.

Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati.

NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda za a yi gwagwarmaya ba tare da an taka doka ba.

Domin Sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwagwarmaya Fafutuka

এছাড়াও পড়ুন:

Artabu Tsakanin ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Banga Ya Ci Rayuka Da Dama A Bauchi

An labarto cewa harin ya wakana ne da safiyar ranar Lahadi kuma ‘yan bindigan sun yi awun gaba da shanu da sauran dabbobin al’umman yankin a yayin farmaƙin.

 

Kazalika, wakilinmu ya gano cewa baya ga ‘yan bijilante da suka rasa rayukansu akwai wasu fararen hula mazauna ƙauyen Sabuwar Sara su ma sun gamu da ajalinsu yayin da suke ƙoƙarin gudun neman tsira bisa harbe-harben ‘yan bindigan.

Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa su ma ɓangaren ‘yan fashin dajin sun rasa mutanensu da dama da ake hasashen sun ma fi ‘yan Bangan mutuwa.

 

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta bayyana haƙiƙanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a ɓangaren ‘yan Banga da ‘yan fashin ba.

 

A sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin, kakakin rundunar , CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 05:40 a ranar 4 ga watan Mayun 2025, inda aka kai rahoton faruwar hakan ga shalkwatar ‘yansanda da ke Alkaleri da ƙarfe 09:40.

 

“Haɗakar ƙwararrun mafarauta daga gundumomin Duguri da Gwana a lokacin da suke aikinsu na sintiri a dajin Mansur, da Dajin Mada, iyaka da jihar Bauchi da jihar Filato, kwatsam sai suka ci karo da tawagar ‘yan fashin daji inda suka musu kwantan ɓauna domin farmaƙarsu,” Wakil ya shaida.

 

Ya ƙara da cewa bisa musayar wuta da aka yi a tsakaninsu, dukkanin ɓangaren sun raunata daga su kansu ‘yan Bijilante da kuma maharan.

 

Kakakin ya ce an tura jami’an ‘yansanda wurin da abun ya faru inda suka kwaso gawarwakin da aka kashe.

 

Binciken farko-farko na ‘yansansa shi ma ya tabbatar da cewa waɗanda suka rasu an samesu ne a dukkanin ɓangarorin biyu har ma wasu fararen hula daga ƙauyen Sabuwar Sara lamarin ya shafa a lokacin da suke neman tsira da rayukansu.

 

Sai dai, rundunar ta ce tunin aka ƙaddamar da bincike domin ganin an kamo ‘yan fashin dajin domin tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a.

 

Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi tur da harin tare da tura jami’ai domin su gana da al’ummar kauyen Mansur domin neman hanyoyin da za a inganta tsaro.

 

Ya jajanta wa iyalan wadanda aka kashe inda ya ba su tabbacin nema musu adalci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zulum Ya Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira 6,000 Garuruwansu A Borno
  • NAJERIYA A YAU: Me Yake Kai ‘Yan Gwagwarmaya Shiga Tasku A Najeriya?
  • ‘Yansanda Sun Kama Matashi Kan Zargin Kashe Mahaifinsa Har Lahira A Jigawa
  • Artabu Tsakanin ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Banga Ya Ci Rayuka Da Dama A Bauchi
  • Umaru ’Yar’adua da shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki
  • Iran Ta Jaddada Cewa: Kungiyoyin Gwagwarmaya Ba Su Karbar Umarni Daga Wani Bangare, Gashin Kansu Suke Ci
  • NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka
  • ‘Yansandan Sun Kama Wanda ake Zargi Da Satar Mutane A Sokoto
  • An kama masu garkuwa da mutane 3 da kuɓutar da wasu