Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin da ke neman tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma
Published: 27th, March 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu.
Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar.
Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar.
Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin bayan cece-kucen da hakan ya haifar a faɗin ƙasar.
Ƙudurorin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke nazari a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.
Aminiya ta ruwaito cewa, majalisar ta janye ƙudirin ne bayan gwamnatocin jihohin sun bayyana adawarsu kan matakin da ke neman tuɓe musu rigar alfarmar da ke bai wa gwamnoni da mataimakansu da kuma mataimakin shugaban ƙasa kariya daga fuskantar tuhuma kan laifuka.
A ranar Larabar da ta gabata ce ƙudirin ya samu karatu na biyu a zauren majalisar, ƙarkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai
এছাড়াও পড়ুন:
SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa
Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane.
Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp