Maniyyata Daga Turai Akan Dawakai Sun Isa Kasar Saudiyya Domin Yin Aikin Hajjin 2025
Published: 4th, May 2025 GMT
Mahajjata hudu – daya daga Maroko sauran kuma daga Sifaniya – sun isa kasar Saudiyya a kan dawakai a wannan makon da ya fice don gudanar da aikin Hajjin 2025, wanda hakan ke tunatar da al’ummar Musulumi tsarin zuwa aikin hajji a shekaru da dama da suka gabata. Mahajjatan sun isa zuwa kasar Saudiyya ne ta kan iyakar Al Hadithah da ke Al Qurayyat, inda jami’an gwamnati suka tarbe su tare da duba lafiyarsu, da kuma basu abubuwan sha don jinjin irin tafiyar da suka yi ta tsawon makonni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu.
Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawaSun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa.
Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki.
Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin daɗin aikinsu.
Aminiya ta ruwaito yadda yajin aikin ya janyo ya haifar da tsaiko ga ayyukan lafiya a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Sun fara yajin ne bayan ƙarewar wa’adin kwana 15 da ƙungiyarsu ta bai wa Gwamnatin Tarayya.
A ranar Asabar ne ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin bayan wani taro ta Intanet da shugabanninta suka gudanar.
A ranar Juma’a, ƙungiyar ta gana da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Ma’aikatar Ƙwadago, Ofishin Shugaban Ma’aikata, Ofishin Akanta-Janar, da Hukumar Albashi da Alawus da wasu ɓangarori na masu ruwa da tsaki domin tattauna buƙatunsu.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, NANNM ta ce ta dakatar da yajin aikin ne bayan duba yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati.
Sanarwar, ta ce gwamnati ta ɗauki matakai masu muhimmanci kuma ta bayar da jadawalin lokacin da za ta cika alƙawuran.
Saboda wannan yarjejeniya da kuma samun masalaha, ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin nan take.
Ta kuma umarci dukkanin ma’aikatan jinya da su koma bakin aiki, tare da gargaɗin cewa ba za ta amince a hukunta kowa ba saboda shiga yajin aikin.
Ƙungiyar ta gode wa mambobinta bisa goyon baya da haɗin kai, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare haƙƙinsu.