Aminiya:
2025-11-03@07:20:55 GMT

Yadda ’yan fashi suka yi wa mafarauta kisan gilla a Bauchi

Published: 5th, May 2025 GMT

’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi.

A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin.

Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Amma ’yan sanad da jami’an Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ba su ce komai ba kan adadin mamatan ba.

Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci jama’a kwantar da hankalinsa, ya kuma kasance a cikin shiri, tare da bai wa ’yan sanda goyon baya wajen gudanar da binciken su.

Kwankwaso: Abba ya mayar wa Baffa Bichi martani Umaru ’Yar’adua da shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka

Wakil ya ce, “A ranar 4 ga watan Mayu, 2025 mun samu rahoto cewa tawagar hadin gwiwar mafarauta daga Duguri da Gundumar Gwana, da ke sintiri a kan hanyar Duguri, Mansur, da dajin Madam da ke kan iyakar jihar Bauchi da Filato, sun yi araba da ’yan fashi, inda a arangamar aka kashe mutane da dama daga bangarorin biyu.

“Mun tura tawagar jami’an tsaro wurin, inda suka gano gawarwakin jami’an tsaro da fararen hula daga kauyen Sabuwar Sara, wadanda ’yan fashin suka harbe su a yayin da suke kokarin tserewa daga harin suka mutu.

“Rundunar ta tura tawaga ta musamman domin kamo duk masu alaƙa da wannan aika-aika.”

Ya kuma ba da  tabbacin cewa za a yi bincike cikin gaskiya da adalci domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban ƙuliya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan fashi mafarauta

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato

Wani magidanci, Malam Jibrin Rabi’u, ya bayyana yadda matarsa, Khadijat Ado, ta ɓace a gidansu da ke unguwar Life Camp a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, sannan kuma aka gano ta a Sakkwato washegari.

Ya shaida wa wakilinmu da yammacin Lahadi, cewa ya dawo gida a ranar Alhamis, sai ya tarar da matarsa ba ta nan.

Malam Jibril ya ce, ya kira wani abokinsa ɗan sanda, wanda ya sanar da ofishin ’yan sanda na Life Camp, Gwarinpa da sauran sassan yankin bayan bincike na farko ya gagara gano inda take.

A cewarsa, na’urar CCTV da ke gidansu ta nuna yadda matarsa ta fita daga gidan cikin natsuwa, har sai da ta fita daga inda kyamarar ke iya ɗauka.

Allah Ya yi wa Malam Nata’ala rasuwa Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a Yobe

Malam Jibrin ya ce duk da ƙoƙarin da suka yi na gano ta a ranar Alhamis ɗin, ba su samu nasara ba.

Sai dai ya ce da yammacin Juma’a aka kira shi aka shaida masa cewa an gano matarsa a Sakkwato, amma ba ta iya magana.

Ya ce, “Yanzu ma har yanzu ba ta iya magana ba, amma ta dawo cikin hayyacinta. Muna tattaunawa ta hanyar rubutu ne kawai.”

Ya bayyana cewa matarsa ta rubuto masa cewa a ranar da ta ɓace, ta ji kamar wani ana kiranta ne, sai ta buɗe ƙofa ta fita — daga nan kuma ba ta san abin da ya faru ba, sai da ta tsinci kanta a Sakkwato.

A cewar Malam Jibrin, “Ta ce da ta isa Sakkwato, ta haɗu da wata mace wadda ta roƙi takarda da biro, sannan ta rubuta mata abin da ya faru domin ba ta iya magana.”

Ya ce daga nan ne wannan matar ta kira shi, inda ya nemi ta da ta kai matarsa wurin danginsa da ke Sakkwato.

Malam Jibrin ya ce har yanzu matarsa tana Sakkwato, kuma ba ta samu damar yin magana ba, amma ya shirya tafiya Sakkwato yau domin ya dawo da ita gida.

Wata majiyar ’yan sanda a Life Camp ya tabbatar da cewa an kawo rahoton ɓacewar a ranar Alhamis, amma ya ce duk wani ƙarin bayani sai an tuntuɓi hedikwatar rundunar.

An kuma bayyana cewa kiraye-kirayen da aka yi wa jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sanda ta Abuja, DSP Josephine Adeh, ba ta ɗaga wayarta ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m