Wani harin makami mai linzami daga Yemen ya fada filin jirgin saman Ben Gurion na Isra’ila
Published: 4th, May 2025 GMT
Dakarun Yeman ta sanar cewa ta kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Falasdinu, a wani mataki na nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da ke fama dake fusnkatar mamaya, zalinci da kisan kare dangi daga Isra’ila.
Kakakin rundunar sojin Isra’ila ya ba da rahoton wani sabon hari da makami mai linzami daga Yeman, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa matsuguni.
Rundunar ta ce ta kunna na’urar tsaronta ta sama domin tinkarar barazanar, amma ta kasa dakile makamin.
Tun ma kafin sanarwar da sojojin Isra’ila suka fitar, kafofin yada labaran Isra’ila sun ba da rahoton kararrakin gargadin makamai masu linzami a yankuna da dama na tsakiyar Falasdinu da ta mamaye.
Daga baya an sanar da cewa an dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen da ke zuwa filin jirgin Ben Gurion.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu.
A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000.
Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp