HausaTv:
2025-11-02@21:10:35 GMT

Kissoshin Rayuwa : Imam Al-Hassan (a) 113

Published: 4th, May 2025 GMT

113-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauransu inda muke masu karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su.

Da fatan masu sauraro zasu kasasnce tare da mu.

///…Madallah, masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da cewa {gwagwarmayar kwace kasar Falasdinu zai fara da tube Mahmood Abbas daga shugabancin kungiyar Kwatar yencin Palasdinawa PLO}.

Shugaba Mahmood Abbas, shugaban gwamnatin jeka na yi ka na Palasdinawa ya dade yana hana ruwa guda a gwagwarmayan da Falasdinawa Musamman a Gaza suke yi don yentar da falasdinawa daga hannu HKI  da wadanda suke taimaka mata. Kuma saboda wadan nan halayensa ya zama shugaban da mafi yawan Falasdina wa basa kaunarsa a yankin Yamma da kogin Jordan ko kuma Gaza.

A ranar Laraban da ta gabata ce, Mahmood Abbas ya kara wulakanta kansa, inda ya dira a kan kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya, dauke da makami da HKI tun ranar 7 ga watan Octoban shekata ta 2023.

A cikin jawabin da ya gabatar a Ramallah da ke yankin yamma da kogin Jordan ‘ya kira yayan kungiyar Hamasa da sunan karnuka, sannan ya bukacesu su mika makamansu ga HKI, su saki fursinonin Fursinonin yahudawan da suke tsare da su a gaza, sannan su mika ikon Gaza gareshi. Wadan nan  bukatun duk na shuwagabannin HKI ga kungiyar Hamas a yakin da suke fafatawa da Hamas a Gaza.

Mahmood Abbass yana son ya maida Gaza, kamar yankin yamma da Kogin Jordan inda yahudawa suke shiga inda suka ga dama a yankin su kuma rusa gidaje da titunan su kuma kama wanda suka ga dama daga cikin falasdinawa a yankin, ba tare da wani ya tanka masu ba.

A wasu lokutan Jami’an yansanda da ke karkashinsa suna kama Falasdinawa su mika su ga yahudawan Isra’ila. Ko su hanasu zanga-zanga, da sauransu. A jawabin bude taron majalisar gudanarwa ta gwamnatin Falasdinawa  (PCC), karo na 32, Mahmood Abbas, ya kira falasdinawan kungiyar Hamas a matsayin, “yayan karnuka”. Wannan majalisar bata gudanar da wani taro bat un shekara ta 2018 sai sau biyu kacal.

Kalaman Mahmood Abbas ga falasdinawa a Gaza, wadanda suka gabatar da shahidai fiye da 52,000 daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023, ba kuskuren harshe bane, don wannan ba kuma shi ne karon farko da yake kiransu da mummunan sunaye ba.

Sannan maimakon ya zabge fushinsa kan shugabannin HKI wadanda suka kashe Falasdinawa fiye da 52,000 da kuma rasa zirin Gaza, Mahmood Abbas ya haw kungiyar Hamas yana zargenta da kare falasdinawa a gaza, ya zarginta da kokarin kare kasar Falasdinu.

Kamar yadda muka bayyana wannan ba shi ne karon farko wanda Mahmood Abbas yake wulakanta Falasdinawa a gaza, musamman kungiyar Hams ba, saboda a cikin watan Mayun shekara ta 2026 a lokacinda yake jawabi a babban zauren MDD ya kirasu “dabbobi”.

Idan har haka ne, kuma shi ne shugaban Falasdinawa, to me ya sa ba zai kubutar da su ba?, don shi mutum ne ko? , to me yasa ba zai kare dubbobinsa ba? Ai dabbobi ma suna bukatar kariya daga maisu.

Wannan zargin da yayi wa dakaron hamas a taron majalisar zartarwan gwamnatin Faladinawa karo na 32 a Ramallah, ya fusata mutane da dama a duniya, sannan bayyana matsayinsa dangane da mutanen da yakamata a ci yana wakiltansu da yardarsu.  

Da farko dai bayan jawabin Abbas kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta yi All..wadai da shi, sannan ta tir da halayensa na nuna ‘Ko in kula’ kan abinda ke faruwa a yankin Gaza. Ta kuma kara da cewa wannan wata alamace da Abbas yana aiki tare da HKI da kawayenta na nesa da kusa don murkushe Falasdinawa a Gaza.

Kungiyar Hamas wacce ta balle daga kungiyar Fatah ta Mahmood Abbas a shekara ta 2000 zuwa sama, ta kammala da cewa jawabn Abbas a taron gudanarwa na gwamnatin Falasdina a karu na 32  a Ramalla, ya nnuna cewa ya gaza hada kan Falasdinawa, kuma ba zai iya kare mutanensa daga baranar HKI ba.

Falasdinawa suna kara ganin Abbas a matsayin matsala ga tafarkin y’entar da  Falasdinawa a maimakon shugaba. Masu sukansa suna cewa, tabbas yana hada kai da HKI don tabbatar da shugabancinsa a kan al-ummar falasdinu da karfi, don ya ci gaba da raba kan Falasdinawa, maimakon ya hada kansu, da haka kuma zai jefe rauni a cikin tafarkin Falasdinawa masu gwagwarmaya a dai dai lokacinda suka fi bukatar hadin kai da kuma karfafasu.

An kafa gwamnatin Falasdinawa wata (FA) ne a bayan yarjeniyar Oslo a shekara ta 1994. Sannan daga bayan shugaban kungiyar PLO na lokacin Yasar Arafat ya zama shugaban gwamnatin Falasdinawan, wanda aka dauka gwamnatin falasdinawa ne na wucin gadi a yankin yamma da kogin Jordan, Qudus da kuma Gaza. Kuma ana gidan gwamnatin Falasdinawa a Rammala a lokacin wani mataki ne na kafa kasar Falasdinu mai cikekken yanci a yankin.

Bayan gazawar tattanawar Camp Devid a shekara ta 2000 wajen bawa falasdinawa yenci, da kuma shigar ‘Ariel Sharon’ firaiministan HKI na lokacin, masallacin Al-aksa, ya ingiza boren Intifada na biyu, wanda ya kai ga sojojin yahudawan suka kashe Falasdinawa akalla 3000 kafin ta lafa. A sannane kuma Mahamood Abbas ya fara bayyana a matsayin dan siyasa a cikin Falasdinawa.

Sannan a shekara ta 2003 shugaban kasar Amurka na lokacin George Bush ya takurawa shugaba Arabafad ya nasa Mahmood Abbas a matsayin Firai minista a gwamnatinsa sa, daga karshe ya amince.

Amma ra’ayin Abbas na hana falasdinawa daukar makami, kamar yadda ya faru a intifada na biyu,  da kuma ra’ayinsa na tattaunawa da yahudawan ya sa falasdinawa da dama suka ki shi. Daga karshe Abbas bai da zabi sai ya sauka daga mukamin Firai minister a cikin watan satumban shekara ta 2003.

Amma a shekarar da ta biyo, 2004, sai shugaba Yasar Arafat ya rasu, sannan a shekara ta 2005 Mahmood Abbas ya zama shugaban gwamnatin falasdinawa, don haka Amurka da sauran kasashen yamma suka sa shi a gaba yana masu aiki a cikin falasdinawa, tare da ra’ayinsa na gwagwarmaya ba tare da daukar makami ba.

Abba baya goyon bayan daukar makama kan HKI, shi yasa yana shiri da kungiyar Hamas wacce ta sami nasarar korar yahudawan HKI daga gaza a shekara ta 2005, kuma tun lokacin ne HKI ta yi mata kofar rago take hana shigowar koma zuwa yankin sai abinda ta amince daga Kofar shiga yankin da ke Rafah da kuma Karim Abu salim.

Don haka tun lokacinda Abbas ya zama shugaban gwamnatin Falasdinawa a Ramalla yake hana Falasdinawa daukar makami, wanda kuma shi ya sa yahudawan suke cin karensu ba babbaka a yankin.

Sannan saboda wannan Ra’ayinsa yahudawan sahyoniya suke shiga yankin yamma da kogin Jordan su kama falasdinawa su kashe wadanda suka ga dama idan wani daga cikinsu ya fidda makami yar ama yansandan Mahmood Abbas su taimaka sojojin yahudawan su kama shi su tafi da shi. Ko su kashe shi. Ba Ruwansa da batun fursinoni falasdinawa fiye da 10,000 wadanda HKI take tsare da su a gidajen yarinta.

Wato muna iya cewa yansandan Mahmood Abbas yansanda yahudawan ne da rigar falasdinawa. A yakin tufanul Aksa a cikin watan Octoban shekara ta 2023 yansandan Mahmood Abbas sun kai sumame kan sannanun garuruwan yamma da kogin Jordan inda yake da iko, kamar Jinin, inda suka kama Falasdinawa da dama wadanda suke dauke da makami .

Hakama a lokacinda falasdinawa a Jenin da kuma yankin sansaninsa suka fara fitowa don fuskantar sojojin yahudawan a shekara ta 2024, yansandan Mahmood Abba sun sake dirar mikaya a kansu. Bayan fafatawa da Falasdinawa a jenin yansandan sun kai farkami a asbitocin yankin inda suke kashe falasdinawa wadanda aka jiwa Rauni a fafatawar.

Sannan bayan haka ne da kadan ne sojojin yahudawan suka fara wani gagarumin Shirin yaki da Falasdinawan da suke dauke da makami a yankin yamma da kogin Jordan. Sannan bayan haka ne sojojin yahudawan suka fara amfani da tankunan yaki da motocin Buldoza suna shiga garuruwan Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan. Suna ruda gidaje duna lalata tituna a garuruwa da dama.

MDD ta bayyana cewa sojojin yahudawan sun kori Falasdinawa a sansanoninsu dake yamma da kogin Jordan har kimani 40,000.

Al-amarin ya kaiga yansandan Mahmood Abbas suna taimakawa sojojin yahudawa fiye da yadda suke taimakawa Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan musamman a sansanin yan gudun hijira na Jenin.

Tun lokacinda kungiyar Hamas ta fara yakin Tufanul Aksa Mahamooda Abbas ya fara takurawa Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan don kwace makamansu, a dai dai lokacinda sojojin yahudawan a karon farko suka fara amfani da jiragen yaki don kashe masu gwagwarmaya da makami a yankin.

A lokacinda kungiyar Hamas ta lashe zaben da aka gudanar a yankin yamma da kogin Jordan da Gaza, a shekara ta 2006. Mahmood Abbas ya hada kai da Amurkawa da kasashen yamma a shekara ta 2007 don kifar da gwamnatin domocradiyya wanda Hamas take jagoranata a Gaza, amma sai suka hadu da maida martini mai tsanani daga kungiyar Hamas, suka lalata makircin kifar da gwamnatin na Hamas karkashin Firai minister Shahid Isma’il Haniyya. Mahmood Abbas bai tama nuna damuwarsa da hana shigo da abinci a zirin Gaza kimani watanni 2 da suka gabata ba.

Masu sauraro saboda kurewar lokaci a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All.ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a yankin yamma da kogin Jordan kungiyar Hamas wacce ta yansandan Mahmood Abbas gwamnatin falasdinawa gwamnatin Falasdinawa sojojin yahudawan su falasdinawa a yankin Falasdinawa a yankin falasdinawa a gaza shugaban gwamnatin Falasdinawa a gaza falasdinawa a Gaza Falasdinawa a Gaza Mahmood Abbas ya ya zama shugaban Falasdinawa da falasdinawa da da Falasdinawa da falasdinawa falasdinawa A wadanda suka a shekara ta masu sauraro

এছাড়াও পড়ুন:

Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya

Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta bayyana shugabar kasa mai ci Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar.

Shugaban hukumar zaben ya ce Shugaba Samia ta yi nasara a zaben da kashi 98% na jimillar kuri’un da aka kada.

Bayanai sun ce manyan ‘yan takarar adawa ba su shiga ba, wasu kuma an tsare su ko kuma an hana su tsayawa takara, wanda hakan ya haifar da tashin hankali.

Jam’iyyar adawa ta kasar ta ce daruruwan mutane ne suka mutu sanadiyyar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki ana yi tun bayan zaben na ranar Laraba.

Wani mai magana da yawun jam’iyyar adawa ta Chadema ya shaida wa AFP cewa kimanin mutane 700 ne suka mutu, a alkalumman da aka tattara daga asibitoci.

Gwamnatin Shugaba Samia ta musanta duk wani “yin amfani da karfi fiye da kima,” yayin da Ministan Harkokin Waje Mahmoud Thabit Kombo ya shaida wa Al Jazeera cewa babu “bayani” kan adadin wadanda suka mutu.

Hukumomin sun katse hanyar intanet, sun sanya dokar hana fita, kuma sun takaita ‘yan jarida, wanda hakan ya takaita samun bayanai.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
  • Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa