Aminiya:
2025-11-02@17:17:25 GMT

Kotu za ta rataye matashi kan kisan karuwa

Published: 5th, May 2025 GMT

Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kan laifin kashe wata karuwa bayan ya yi lalata da ita.

Babban Kotun Jihar Ekiti ce ta yanke masa hukuncin bayan an gurfanar da shi kan zargin haɗa baki da kuma garkuwa da matar da kuma amfani da maganin kashe ciyawa wajen halaka ta a ranar 18 ga Afrilun 2024.

Tun da farko mai gabatar da ƙara, Ibironke Odetola, ya bayyana wa kotun a ranar 6 ga watan Fabrairu, cewa wanda ake zargin ya haɗa baki d da wani abokinsa wajen sace matar da ke sana’ar kasuwanci.

Wanda ake zargin, David Isaiah, mai shekara 26, ya shaida wa kotun cewa bayan ya yi lalata da matar ne ya yi amfani da wayarta ya kira abokan sana’arta da cewa an yi garkuwa da ita, sai an kawo kuɗin fansa Naira 100,000.

Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato Umaru ’Yar’adua da shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki

A yayin da yake karanta hukuncin, Mai Shari’a Lekan Olatawura, ya yanke wa wanda aka gurfanar da laifin garkuwa da mamaciyar.

“Don haka an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 21 kan laifin haɗin baki kan laifin garkuwa da mutane. Game da laifin kisa kuma kotu ta yanke mas a hukuncin ratayewa har sai ya mutu,” in ji alƙalin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Garkuwa Karuwa Rataye

এছাড়াও পড়ুন:

Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka

Wasu lauyoyi biyu a Najeriya sun gargaɗi Gwamnatin Tarayya da ta yi taka-tsantsan wajen yin hulɗa da ƙasar Amurka, inda suka ce maganganun Amurka a kan Najeriya abun ruɗarwa ne 

Babban lauyan nan, Cuf Okoi Obono-Obla, wanda tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara ne, ya zargi Amurka da son raba kan ’yan Najeriya da sunan kare Kiristoci.

Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 

Ya ce iƙirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya ƙarya ne face nufin tayar da hankali da kawo rikici.

“Najeriya ba ta taɓa zama barazana ga zaman lafiyar duniya ba,” in ji Obono-Obla.

“Idan Amurka, inda ake yawan harbe mutane a coci-coci, ba ta gayyaci sojojin ƙetare su shigo musu ba, to kamata ya yi ta bar Najeriya ta magance nata matsalolin.”

Ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin Amurka na yin katsa-landan cikin harkokin Najeriya zai zama take doka da tauye ikon ƙasa.

Shi ma Barista Leonard Anyogo, kuma shugaban ƙungiyar ‘Good Governance Advocacy International’, ya shawarci Najeriya da ta bi hanyoyin diflomasiyya wajen mayar wa Amurka martani ba da faɗa ba.

“Ya kamata mu tattauna, ba mu yi fada ba,” in ji Anyogo.

“Najeriya ta nemi haɗin kai da Amurka a fannin tsaro da diflomasiyya domin kare muradunta.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara