Rahotonni na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai kashe dakaru huɗu yayin wani hari da suka kai sansanin soji a Jihar Yobe.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙaddamar da hari kan sansanin soji na “27 Task Force Brigade” da ke garin Buni Yadi, a yankin Ƙaramar Hukumar Gujba da tsakar daren Asabar.
Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a SakkwatoHarin na zuwa ne kwana guda bayan Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabashin ƙasar sun gudanar da taro a Damaturu, babban birnin jihar da nufin magance matsalolin yankin, ciki har da matsalar tsaro.
A baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram da na ISWAP na neman dawo da hare-hare a yankin.
A cikin makon nan ma ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin wani hari da yayi sanadin mutuwar mutum 26 a Jihar Borno.
Ko makonni biyu da suka gabata sai da mayaƙan Boko Haram suka kai hari sansanin soji da ke yankin Chalie a Ƙaramar Hukumar Buni Yadi, inda suka kashe dakaru uku.
Sai dai a bayan nan ne Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ƙwato dazukan Arewa da ma sauran sassan ƙasar daga hannun masu garkuwa mtane domin karɓar kuɗin fansa da ‘yan ta’adda
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dakaru Jihar Yobe
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara
Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbar shi da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan dawowarsu ofis.
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara na tsawon watanni shida a lokacin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a jihar.
Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50mSai dai a ranar Laraba, Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci tare da umartar gwamnan, mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar da su koma bakin aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba.
A halin yanzu, tsohon shugaban riƙon ƙwarya na jihar, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya miƙa mulki a hukumance ga Gwamna Fubara.
Hotunan yadda magoyan suka taru: