Sharhin bayan Labarai: Ci Gaban Harkokin Kasuwanci Tsakanin Iran Da Kasashen Waje Duk Tare Da Takunkuman Kasashen Yamma
Published: 5th, May 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta.
////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata, sannan take barazanar zata farwa kasar da yaki saboda shirin na makamashin nukliya, sabbin rahotanni sun bayyana cewa iran tana gaba a fitar da kayaki kasuwanci zuwa kasar China sannan ita ce ta 9 a duniya wajen samar da kwan kaji da sauran tsuntsaye.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa, yawan danyen man fetur wanda kasar Iran take sayarwa kasar China kadai ya kai ganga miliyon 1.8 a ko wace rana a cikin watan Mayun da ya gabata na wannan shekara ta 2025.
Labarin ya kara da cewa kasar Iran a halin yanzu tana sayarwa kasashe 110 kayakin abinci na halal, wadanda suka hana da nama da sauran kayakin abincin na dabbobi. Kuma ita ce kasa ta 9 a duniya wajen samar da kwan suntsaye.
A wani labarin kuma yankin ciniki mara shinge na Aras ya samar da kudaden shiga ga kasar wanda ya kai dalar Amurka miliyon $200 a shekara ta 2024 da ta gabata. Hadi Moghaddamzadeh, shugaban yankin ya bayyana cewa yankin nasa ya samar da kudaden shiga hard alar Amurka miliyon 200, a arewa maso yammacin kasar kuma kudaden shigan da aka samu daga kasar Azerbaijan kadai ya kai dalar Amurka miliyon 11.
A lokacinda yake magana da kamfanin dillancin labaran Pars today a gefen kasuwar baje koli na Iran Expo 2025 wanda aka gudanar a nan Tehran Moghaddamzadeh ya kara da cewa yankin ciniki mara shingen na Aras ya fi muhimmanci a kan sauran iran wannan yankunan da ake da su a nan kasar Iran, saboda wuraren yawon bude ido da shakatawa da yankin yake da su.
A bangaren sayar da kayakin abinci wanda ake kira Halal kuma, shi ne kayakin da iran take fitarwa zuwa kashe kimani 110 a duniya, kuma yake gaza da wasu kasashe a wannan bangaren.
Darakta mai kula da wannan bangaren, ya ce kayakin abinci na Halal wadanda suke fita daga kasar Iran suna zuwa kasashen kamar Malaysia, Singapore, kasashen yankin tekun farisa, arewacin Africa da sauransu.
Ya ce a yankin dai kayakin abinci daga Iran suna shiga kasashen Iraq, Turkiyya, UAE, Afghanistan, Russia, da wasu kasashen Turai.
Sannan shugaban kwastom na Jolfa, ya bayyana cewa a watan da ya gabata, kayakin abince na kimani dalar Amurka miliyon 8.5 suka fita da kofar fitar da kayaki kasuwanci a yankinsa a watan da ya gabata kadai.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kayakin abinci bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su. Sai dai a lokacin, hukumomi masu kula da harkokin kasa da kasa, kamar su Hukumar Lafiya ta Duniya, da Majalisar Dinkin Duniya dukkansu sun kasa tilasta musu sauya manufofinsu. Wannan tsarin kasa da kasa, idan mun bar shi haka ba tare da wani sauyi ba, to, wata rana za mu ga an koma tsarin zalunci na zamanin mulkin mallaka, wanda zai yi barazana ga hakkin rayuwa, da raya kai na al’ummar kasashe masu tasowa. Ta haka za mu san cewa gyara ya riga ya wajaba.
Saboda haka, shawarar inganta jagorancin duniya ta zama wani abun dake biyan bukatun dake akwai a duniyarmu. Wannan ya sa ta samun karbuwa a tsakanin kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. Inda shahararren dan jarida a Najeriya Lawal Sale, ya rubuta a cikin wani sharhinsa cewa, “Wannan shawara za ta haifar da karin kwanciyar hankali, da tabbas a duniyarmu mai cike da tashin hankali, musamman ma a nahiyar Afirka.” Kana a nasa bangare, Paul Frimpong, wani shehun malami dan kasar Ghana, ya ce shawarar nan “tana tabbatar da cewa tsarin jagorancin duniya ba zai ci gaba da zama karkashin mallakar wasu kasashe masu karfi ba.” Kana dan jaridar kasar Lesotho, Silence Charumbira, ya ce shirin na baiwa kananan kasashe damar zama masu hakikanin ‘yancin kai.
Ta wannan shawara ta inganta jagorancin duniya, za mu iya kara fahimtar halayyar kasar ta Sin. Ko da yake wani yanayin da duniyarmu ke ciki shi ne dishewar tauraron kasashen yamma, amma duk da haka, kasar Sin ba ta neman yin koyi da kasashen yamma wajen yin babakere a duniya. Tana neman gyara, da inganta tsare-tsaren kula da harkokin duniya, ta yadda za ta tabbatar da moriyar dukkan kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, maimakon kafa wani sabon tsari da ya saba wa tsarin kasa da kasa na yanzu. Dalilin da ya sa haka shi ne babban burin kasar Sin ta fuskar diflomasiyya, shi ne kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil’adama, da kokarin tabbatar da ci gaban harkokinsu na bai daya.
Yayin da karin kasashe ke nuna goyon bayansu ga shawarar kula da al’amuran duniya da kasar Sin ta gabatar, tabbas za mu shaida hadin gwiwar karin mutane a duniya don neman wanzar da adalci, abin da zai haifar da damar tabbatar da daidaito da adalci a duniyarmu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp