An Kama Wani Ɗan Ghana Bisa Zargin Kai Mata Hajji Ba Tare Da Lasisi Ba
Published: 5th, May 2025 GMT
Rundunar tsaron dake lura da aikin Hajji ta kama wani ɗan ƙasar Ghana bisa zargin ƙoƙarin fitar da mata huɗu daga ƙasashen waje zuwa Makkah ba tare da lasisin Hajj ba.
Matan, waɗanda ke cikin mota, an yi amfani da ɗakin kaya na motar domin ɓoye su don gujewa dokokin Hajj.
Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya Maniyyata Daga Turai Akan Dawakai Sun Isa Kasar Saudiyya Domin Yin Aikin Hajjin 2025Rundunar tsaron ta kama direban motar tare da mata huɗun, sannan aka miƙa su ga hukumar da ta dace don aiwatar da hukuncin doka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kasar Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan kungiyar asiri: Mutum 95 sun shiga hannu a Edo
Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama mutane 95 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri.
An kama mutanen ne a wani farmaki da aka kai kan masu aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin asiri a garin Benin City da kewaye a makon da ya gabata.
Kwamishinan ’yan sanda, Monday Agbonik, ya bayyana cewa an gurfanar da 64 daga cikin wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyoyin Maphites, Eiye, da Aye kuma ake zarginsu da kisan gilla da aka yi kwanan nan a rikicin kungiyoyin asiri.
Kayan da aka ƙwato sun hada da bindigogi biyu ƙirar gida, bindiga guda mai tashi daya, da harsashi 24.
’Yan sandan sun shawarci iyaye da su kula da ayyukan ’ya’yansu kuma sun gargadi matasa da kada su shiga kungiyoyin da ba bisa ka’ida ba wadanda ke kawo hatsari ga rayuwarsu.
Bincike na ci gaba da gudana kan sauran wadanda ake zargin.