Sojojin Sun Kakkabe Wasu Manyan ‘Yan Bindiga A Zamfara
Published: 4th, May 2025 GMT
Rundunar sojojin Najeriya ta 1 karkashin jagorancin Birgediya Janar Timothy Opurum ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi da ta’addanci da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, musamman a kananan hukumomin Talata Mafara da Kaura Namoda.
A wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kyaftin Sulaiman Omale ya fitar tace a farkon farkon watan Mayun 2025, dakarun su da ke sintiri na yaki sun ci karo da dimbin ‘yan ta’adda da suka kutsa kai kauyen Mai Kwanugga a karamar hukumar Talata Mafara.
Ya yi bayanin cewa, ‘yan ta’addan sun rika kai hari kan mutanen yankin tare da kona gidaje kafin isowar sojojin, inda ya ce, bayan tuntubar rundunar, sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan bayan barin wuta, inda suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama, ciki har da fitattun ‘yan ta’addan guda biyar da suka hada da Auta Jijji, Dankali, Sagidi, Kachallah Rijaji, da Kachallah Suza.
Sanarwar ta kuma ce, dakarun rundunar 1 sun bi sahun ‘yan ta’addan da suka tsere, inda aka samu nasarar kwato wasu tarin makamai da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda 4, Bindigan PKT 1, bututun RPG guda 2, bama-baman RPG guda 6, harsasai 28 na 7.62mm harsashi na musamman na PKT 3 da harsasai na musamman na PKT 3.
Birgediya Janar Timothy Opurum ya yabawa kwazon sojojin tare da tabbatar wa ‘yan kasar tabbacin da rundunar ta yi ba tare da bata lokaci ba na maido da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Rundunar sojin Najeriya ta karfafa gwiwar jama’a da su ci gaba da bayar da sahihin bayanai ga hukumomin tsaro tare da kaucewa daukar doka a hannunsu.
REL/AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Tsaro Zamfara yan ta addan
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Saman Yakin Sojojin Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Siriya
Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankunan birnin Damascus fadar mulkin Siriya da kuma yankin yammacin kasar
Majiyoyin cikin gida na kasar Siriya sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan sansanonin sojin Siriya bayan da suka yi shawagi a kan garuruwan Hama, Dar’a, Damascus, yankin kan iyakar Siriya da Lebanon da kuma gabar tekun Siriya.
Wadannan su ne fitattun abubuwan da suka faru a lokacin da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wa kasar Siriya hare—haren wuce gona da iri a yammacin ranar Juma’a.
Rahotonni sun kara da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare guda biyu kan birnin Al-Tall da ke cikin karkarar Damascus, sannan sun kai wasu hare-hare guda 6 a wajen babban birnin kasar, Damascus, yayin da jiragen yakin ‘yan mamayar suke ci gaba da shawagi a sararin samaniyar Dar’a, As-Suwaida, da Quneitra.