An Kammala Horon Hadin Gwiwa Tsakanin Sojojin Saman Sin Da Masar Cikin Nasara
Published: 6th, May 2025 GMT
Da safiyar jiya Lahadi bisa agogon wurin, aka kammala horon hadin gwiwa tsakanin sojojin saman kasashen Sin da Masar mai suna “Shaho na wayewar kai-2025” cikin nasara, a wani sansanin sojojin saman Masar, wanda ya kwashe kwanaki guda 18.
Wannan horon na hadin gwiwa shi ne karo na farko da rundunar sojin saman kasar Sin ta aike da dakaru zuwa kasashen Afirka domin ba da horon hadin gwiwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Ghana Za Ta Hada Gwiwa Da Gwamnatin Jihar Kebbi Kan Noma
Ministan Abinci da Noma na Jamhuriyar Ghana Mista Eric Opoku, ya ce Ghana za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Kebbi domin bunkasa noman shinkafa a kasarsa.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar a Birnin Kebbi.
Ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin Ghana da ta fara aiki watanni hudu da suka gabata, tana neman hanyoyin magance kalubalen samar da abinci a kasar.
A cewar Ministan, sabuwar gwamnatin ta gaji wani katafaren kudi na shigo da kaya inda ta ke shigo da shinkafa da yawa duk kuwa da kasa mai albarka da ruwa mai yawa, wanda zai iya tallafawa noman cikin gida.
Mista Opoku ya yi nuni da cewa, kasar Ghana ta samu kwarin gwuiwa ne sakamakon nasarar da jihar Kebbi ta samu a fannin noman shinkafa, wanda shi ne babban makasudin ziyarar da suka kai.
Da yake mayar da jawabi, mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar, a lokacin da yake maraba da tawagar kasar Ghana tare da nuna sha’awarsu na hadin gwiwa a fannin noma da gwamnatin jihar Kebbi, ya bayyana cewa jihar a shirye take ta hada kai da kasar Ghana, musamman a fannin noma.
Ya ce, baya ga aikin noma, jihar ta samu albarkar ma’adanai irin su Zinariya da Lithium, wadanda a shirye suke don bincike.
COV/Abdullahi Tukur