Kasar Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wani Hari Da Zata Fuskanta Daga Makiya
Published: 5th, May 2025 GMT
Ministan Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Za su mayar da martani mai tsanani da karfi kan duk wani ta’addanci da kasarsu za ta fuskanta
Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake mayar da martani ga barazanar Amurka, ya tabbatar da cewa Iran za ta mayar da martani mai karfi tare da kai hare-hare kan dukkanin wasu muradun Amurka da sansanoninta da suke wannan yankin.
Birgediya Janar Nasirzadeh ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da tarin makamai masu linzami, kuma idan aka kakaba mata yaki, to za ta yi amfani da su ba tare da bata lokaci ba, ko kuma a duk kan muradun makiya.
Ministan ya jaddada cewa: “Ba su da wata kiyayya da kasashe makwabta, amma tabbas idan sansanonin Amurka suka kai hari kan Iran, to lallai muradintaa duk inda suke zasu fuskancin hare-haren daukan fansa,” yana mai cewa: Makami mai linzami na Qasem Basir yana da juriya a fagen yakin na’ura mai kwakwalwa kuma yana iya ketare tsarin makamai masu linzami.”
Ya bayyana cewa: “makamin na Qasem Basir yana da saukin sarrafawa tare da cimma wurin da aka harba shi a kowane yanayi saboda sabon tsarin ci gaban da ya samu da kuma yadda aka sarrafa jikin sa da sinadarin carbon fiber, wanda ke kubuta daga makamai masu linzami da na’urorin radar.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.