Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-03@10:55:43 GMT

Ghana Za Ta Hada Gwiwa Da Gwamnatin Jihar Kebbi Kan Noma

Published: 4th, May 2025 GMT

Ghana Za Ta Hada Gwiwa Da Gwamnatin Jihar Kebbi Kan Noma

Ministan Abinci da Noma na Jamhuriyar Ghana Mista Eric Opoku, ya ce Ghana za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Kebbi domin bunkasa noman shinkafa a kasarsa.

 

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar a Birnin Kebbi.

 

Ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin Ghana da ta fara aiki watanni hudu da suka gabata, tana neman hanyoyin magance kalubalen samar da abinci a kasar.

 

A cewar Ministan, sabuwar gwamnatin ta gaji wani katafaren kudi na shigo da kaya inda ta ke shigo da shinkafa da yawa duk kuwa da kasa mai albarka da ruwa mai yawa, wanda zai iya tallafawa noman cikin gida.

 

Mista Opoku ya yi nuni da cewa, kasar Ghana ta samu kwarin gwuiwa ne sakamakon nasarar da jihar Kebbi ta samu a fannin noman shinkafa, wanda shi ne babban makasudin ziyarar da suka kai.

 

Da yake mayar da jawabi, mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar, a lokacin da yake maraba da tawagar kasar Ghana tare da nuna sha’awarsu na hadin gwiwa a fannin noma da gwamnatin jihar Kebbi, ya bayyana cewa jihar a shirye take ta hada kai da kasar Ghana, musamman a fannin noma.

 

Ya ce, baya ga aikin noma, jihar ta samu albarkar ma’adanai irin su Zinariya da Lithium, wadanda a shirye suke don bincike.

 

COV/Abdullahi Tukur

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: jihar Kebbi

এছাড়াও পড়ুন:

Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.

Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.

Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin  noma daban daban.

A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.

Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.

Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.

Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.

Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.

Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.

Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam  yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.

Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.

A garin Chuwasu  dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.

Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.

Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.

Yace da farko suna da shakku akan amfani  da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.

Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.

Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar  Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.

A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.

A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.

Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.

Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda