Yayin da aka tabo batun manufofin cinikayya da gwamnatin Trump ta dauka, Newsom ya ce, dalilin da ya sa ya soki matakan na gwamnatin Trump shi ne, jihar California ta fi fama da mummunan tasirin da manufofin suka haifar sama da sauran jihohin kasar.

 

Tun bayan da shugaba Trump ya sanar da matakin kakaba haraji a watan Afirilu, Newsom ta yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki da ke wajen Amurka, da kada su sanya harajin ramuwar gayya kan kayayyakin da ake fitarwa daga jihar California.

Kazalika, California ce jihar farko da ta kai karar gwamnatin Trump kan batun harajin. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar

Daga Usman Mohammed Zaria

Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu.

Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa.

A cewarsa, Birnin Kudu za ta amfana da gina hanyoyi masu tsawon kilomita 113, wanda ya hada da hanyoyin kauyuka da wadanda ke hada al’umma da sauran sassan jihar.

Dr. Uba ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen saukaka zirga-zirga, inganta harkokin tattalin arziki da samun sauki ga muhimman ayyuka ga jama’a.

Ya bayyana tabbacin cewa za a dade ana cin moriyar aikin hanyoyin,  tare da hanzar ayyukan ci gaba da bunkasar karamar hukumar.

Shugaban ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya da cigaba a Birnin Kudu tare da yin alkawarin ci gaba da hada kai da gwamnatin jiha domin tabbatar da cewa jama’a suna amfana da fa’idodin dimokuraɗiyya.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai