Gwmana Lawal Ya Bayyana Wa UNICEF Shirin Jihar Zamfara Na Ƙaddamar Da Dokar Kare Al’umma
Published: 26th, January 2025 GMT
“Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni.
“Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara da walwalarsu.
“Dokar nakasassu ta jihar Zamfara ta nuna ƙudurinmu na kare haƙƙin nakasassu. Wannan na neman kawar da wariya da haɓaka damar shigarsu cikin al’umma. Mun haɗa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da nakasassu, don tabbatar da jin muryoyinsu.
“Saboda haka, za a sake duba dokar don ƙara haɗa kai, kuma za a kafa kwamitin da zai magance takamaiman buƙatun nakasassu.”
Gwamna Lawal ya ƙara jaddada cewa gwamnatinsa ta tsinci fannin kiwon lafiya a cikin wani mawuyancin hali a jihar.
“Don cimma burinmu na samar ingantacciyar kiwon lafiya kuma mai araha daidai da tsarin duniya, mun ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya.
“Misali, ta hanyar Hukumar Raya Al’umma da Ci Gaban Jama’a (CSDA), gwamnatin jihar ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 61, ciki har da manyan asibitoci 10, sannan ta shiga tsakani a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 51.
“Tare da tallafin gwamnatin jiha kai tsaye, mun gyara tare da inganta asibitin ƙwararru na Yariman Bakura da manyan asibitocin Talata Mafara da Shinkafi, inda muka mayar da su Manyan Asibitocin Ƙwararru na yankin.
“Mun kuma fara gina cibiyar VVF don kula da matsalolin mata masu juna biyu tare da amincewa da gina cibiyar gwaje-gwaje a matsayin wani bangare na ƙudurinmu na samar da ingantaccen kiwon lafiya.
“Ƙoƙarin da muke yi, tare da goyon bayan dukkan abokan hulɗarmu, ya riga ya fara samar da sakamako mai kyau a dukkan tubalan gina tsarin kiwon lafiya.
“Mun yi nasarar dakatar da yaɗuwar cutar shan inna a jihar Zamfara, kuma mun samu raguwar bullar cututtukan da za a iya magance su ta hanyar rigakafi, kamar su kyanda, sankarau, da zazzabin rawaya. A shekarar 2024, jiharmu ta samu bullar cutar Diphtheria guda biyu kacal duk da barkewar annobar a jihohin makwabta.
“Mun kuma ba da gudunmawa sosai wajen gyara Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma da ke Gusau da kuma gyara Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya da ke Tsafe.
Gwamnan ya yaba da haɗin gwiwar UNICEF da jihar, kuma ayyukan sun yi matuƙar tasiri.
“A kan tasirin da GAVI ya yi a jiharmu, muna godiya musamman da yadda ku ka haɗa cibiyoyin kiwon lafiya 50 na mu da na’urorin wutar lantarki masu amfani da hasken rana, wanda ke ba su damar samar da ayyuka na sa’o’i 24 cikin inganci.”
“Wannan aikin yana haɓaka ƙarfinmu don adanawa da rarraba alluran rigakafin zuwa wurare daban-daban. Zuba jarin ku a rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da ban-ɗakuna a cibiyoyin kiwon lafiya 29 yana inganta jin daɗin ma’aikata da marasa lafiya, yana kuma ƙarfafa alaƙar al’umma ga wuraren kiwon lafiya.
“Muna godiya da goyon bayanku na shigar da mata da yara marasa galihu 33,000 cikin tsarin inshorar lafiya na jihar. Wannan aikin yana ɗaya daga cikin ayyuka mafi tasiri da aka taba yi, kuma mun sadaukar da kai don ci gaba da samun nasarori.”
A farko, Cristian Munduate, wakilin UNICEF a Nijeriya, ya ce wannan ne karo na farko a duniya da GAVI ta yanke shawarar tallafa wa tsarin kiwon lafiya na ƙasa da ƙasa. “Mun yi farin ciki saboda an ga sakamako mai kyau a Zamfara, kuma wannan zai sa GAVI ta ci gaba da tallafa wa ayyukan kiwon lafiya a irin wannan matakin ba kawai a cikin ayyukan ƙasa ba.”
এছাড়াও পড়ুন:
An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
’Yan sanda a jihar Legas sun kama wani tsohon fursuna tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a jerin laifukan fashi da yankan aljihu a jihar kwana biyar da fitowa daga kurkuku.
Tsohon fursunan mai shekaru 25 da haihuwa, Segun Kolawole, an kama shi ne bayan kwana biyar da aka sako shi daga cibiyar gyaran hali ta Kirikiri, a jihar Legas.
Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano SpalletiSauran wadanda aka kama tare da shi sun haɗa da Sodiq Isa mai shekaru 27 da Adekanmbi Ganiu mai shekaru 21.
Rahotanni sun nuna cewa an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifukan yankan aljihun mutane da sauran laifukan sata a sassa daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da cafke Kolawole, inda ta ce an kama shi da misalin ƙarfe 8 na safiyar Talata a kasuwar Oshodi, bayan jami’ai sun lura da motsinsa da ya zama abin zargi.
Adebisi ta ce an same shi da tsabar kuɗi ₦80,000 da wayar Infinix Note 40 Pro, waɗanda aka gano daga wani fashi da ya aikata a Opebi, inda ake zargin ya saci ₦200,000 da wayar daga hannun wani ɗan kasuwa da ke barci.
“Bincike ya ƙara tabbatar da cewa ya riga ya sayi sabbin kaya da takalma da wani ɓangare na kuɗin da ya sata, waɗanda suma aka kwato su daga hannunsa,” in ji ta.
Haka kuma, a wani samame daban da aka gudanar da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Juma’a, jami’an RRS sun kama Sodiq Isa da Adekanmbi Ganiu bisa zargin yunkurin satar wayoyin hannu daga hannun fasinjoji a sassa daban-daban na Legas.