Ba zan shiga ruɗani ba saboda matsalolin Man United – Amorim
Published: 26th, January 2025 GMT
Ruben Amorim ya yi amai ya lashe kan kalaman da ya yi cewar ƙungiyarsa ta Manchester United ta kakar nan ita ce mafi muni a tarihi.
Sai dai ya ce ba zai yi yaudara ba da cewar ba su da manyan matsaloli ba a kasa.
Amorim ya ce ya yi kuskure da ya samar da baraka lokacin da ya fuskanci ƴan wasa nan take, bayan tashi karawar da Brighton ta yi nasara 3-1 a Premier League.
Hakan ya sa ya gana da ƴan jarida cikin fushi da ta kai ya faɗi wasu kalaman.
An tambaye shi ko ya san cece-kucen da batunsa ya haifar kafin fuskantar Rangers a Europa League, Amorin sai ya ce yana magana da kansa ba da ƴan wasa ba.
Sai dai ya amince da dukkan sakamakon da ya faru a United tun bayan da ya kama aiki a cikin Nuwamba – Ya samu maki 11 da rashin nasara shida daga wasa 11 a Premier League – wannan ba abin a yaba bane.
”Ina magana da kaina fiye da ƴan wasa, kamar yadda Amorim ya ce ”Amma wasu lokutan yana da wuya na ɓoye fushi na.”
United tana gurbin da za ta iya kai wa zagayen ƴan 16 a Europa League kai tsaye, an fitar da ita a League Cup, kuma tana ta 13 a teburin Premier League.
Har yanzu akwai batun da ake tambaya kan dakikin da United ba ta kokari a gida, wadda aka doke wasa huɗu daga biyar da ta yi baya.
An doke United wasa shida daga 12 da ta yi a Old Trafford a Premier League – ƙwazo mafi muni tun bayan 1893-94.
Watakila United ta fuskanci wasannin gaba da kwarin gwiwa, saboda mai tsaron baya, Victor Lindelof ya koma atisaye bayan jinya, haka shima Marcus Rashford ya fara karɓar horo, wanda ake alakanta shi da wasu ƙungiyoyin.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa
Wata koutun soja ta yanke wa wani jami’inta hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifn kashe buduwarsa.
Kotun da ta zauna a Hedikwatar Runduna ta 82 da ke Enugu, ta yanke wa Private Adamu Mohammed hukuncin kisa kan laifin budurwar taas mai suna Hauwa Ali.
Da yake sanar da hukuncin, Shugaban kotun, Birgediya Sadisu Buhari, ya ce, “Kotun Soja ta Kasa ta yanke hukuncin cewa sojan da ake tuhuma, mai lamba 21NA/80/6365 Private Adamu Mohammed, an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa tuhumar kisan kai.”
Mukaddashin kakakin Rundunar, Jonah Unuakhalu, ya ce kwamitin kotun ya cimma matsaya ɗaya bayan nazari mai zurfi na shaidu, tarihin aikin wanda ake tuhuma, da kuma roƙon sassauci daga lauyansa.
Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Kano: Galadima biyu a masarauta ɗaya Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a BornoYa shaida wa manema labarai a Abuja cewa kotun sojan, ta kuma yanke wa wani Soja mai suna Private Abubakar Yusuf hukuncin ɗaurin shekaru 10 a kurkuku saboda samun sa da laifin fashi da makami a wani shahararren kantin sayayya a Enugu.
Ya kara da cewa an yanke wa waɗannan mutane biyu hukuncin ne bayan kammala shari’o’insu kan laifukan kisan kai da fashi da makami.
Babban Kwamandan Runduna ta 82, Manjo-Janar Oluyemi Olatoye, ne ya kaddamar da kotun sojin a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, domin yanke hukunci kan shari’o’in da suka shafi ma’aikatan da suka yi kuskure a cikin Rundunar.
A cewarsa, waɗannan hukunce-hukuncen sai sun samu tabbatarwa daga hukumomin soji da suka dace, wanda ya nuna ƙarshen shari’o’in sojojin.
Ya sake jaddada ƙudurin Sojojin Najeriya na tabbatar da ɗa’a da kuma kiyaye mafi girman ƙa’idoji na ɗabi’u da ƙwarewa.
“Kuskuren ayyukan wasu kaɗan ba su nuna ƙimar ƙungiyar ba. A koyaushe ana ɗaukar matakai masu sauri da kuma ƙarfi don tabbatar da riƙon amana da adalci,” in ji shi.