Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
Published: 6th, May 2025 GMT
Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta
Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke yi, ko da kuwa wani mataki ne da ya sabawa ‘yancin kai, ko cikakken amincin Iran ko kuma muhimman muradun kasa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, za a mayar da martani cikin gaggawa, da ya dace kuma halastacce.
Wannan dai ya zo ne a cikin wata wasika da Amir Sa’ed Irawani, jakada kuma wakilin din-din-din na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya aikewa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya Evangelos C. Sirri dangane da barazana da zargin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi kan Iran.
Irawani ya kuma jaddada cewa: Zai so ya janwo hankali shugabannin Majalisar Dinkin Duniya da kuma hankalin mambobin kwamitin sulhun Majalisar zuwa ga wani gagarumin keta dokokin kasa da kasa da yahudawan sahayoniya suke yi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Jamhuriyar Musulunci ta Iran Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Wa Da Bappa Bichi Martani
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp