Nijeriya Ta Yi Asarar Naira Biliyan 118 Sakamakon Barnatar Da Iskar Gas A Watanni 2
Published: 4th, May 2025 GMT
A cewar hukumar, kamfanonin mai da iskar gas da ke aiki a kasar sun samar da iskar gas na naira biliyan 22.3 daga ayyukansu na teku.
Hukumar ta lissafa asarar ta amfani da Babban Bankin Nijeriya (CBN) na musayar canji na naira 1,520 zuwa dala daya.
Hukumar kula da muhalli ta lura cewa yawan iskar gas da ya tashi daga bangaren teku na masana’antar a watan Janairu da Fabrairu, ya ba da gudummawar tan miliyan 1.
A daidai wannan lokacin a cikin 2024, kamfanonin mai da iskar gas da ke aiki a bakin teku sun fitar da iskar gas 29.2 BSCF, darajar dala miliyan 102.3 (N155.496 biliyan); tare da takunkumin da aka biya na dala 58.4 (N88.768 biliyan); fitar da carbon diodide’ na tan miliyan 1.6 da yuwuwar samar da wutar lantarki na 2,900 GWh.
Hukumar ta bayyana cewa jimlar 71.0 BSCF na iskar gas da kamfanonin mai da iskar gas suka fitar a cikin watanni biyu na 2025 sun ba da gudummawar tan miliyan 3.8 na iskar ‘carbon diodide’ zuwa sararin samaniya; kuma yana da damar samar da 7,100 Gigawatts na wutar lantarki.
“Kamfanonin da suka gaza suna da alhakin biyan takunkumi na dala miliyan 141.9, kimanin naira biliyan 215.688,” in ji rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da iskar gas iskar gas da
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Kakabawa Kamfanonin Da Suka Hulda Da Iran Bangaren Man Fetur
A dai-dai lokacin da kasashen Amurka da JMI suke ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliya ta Iran gwamnatin Amurka a jiya Laraba ta dorawa kamfanoni da mutanen da suke mu’amala da JMI a bangaren man Fetur takunkuman tattalin arziki. Da dama daga cikin wadannan kamfanoni na kasar China ne.
Jaridar ‘the Nation’ ta Amurka ta ce tun farkon wannan shekarar ne shugaban Trump ta farfado da takurawar tattalin arziki mafi muni a ka kasar Iran da nufin tilasta mata dawowa teburin tattaunawa ko kuma ta wagaza cibiyoyin Nukliyar kasar.
A halin yanzu dai kasashen biyu zasu ci gaba da tattaunawar ba kai tsaye ba, karo na hudu a birnin Roma na kasar Italiya a ranar Asabr mai zuwa. Kuma mai yuwa daga karshe su samarda sabuwar yarjeniya a tsakaninsu, kuma akwai yiuwar su kasa yin haka.
Wannan kuma zai faru ne idan Amurka ta bukaci JMI ta daina mu’amala da sinadarin Uranium kwatakwata ko kuma ta shigar da wata bukata wacce Iran ba zata amince ba.