Iran Ta Jaddada Cewa: Kungiyoyin Gwagwarmaya Ba Su Karbar Umarni Daga Wani Bangare, Gashin Kansu Suke Ci
Published: 5th, May 2025 GMT
Iran ta mayar da martani kan zargin da ake mata game da alakar ta da Yemen tana cewa; Taimakon da Yemen ke yi wa Falasdinu hukunci ne mai cin gashin kansa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa dangane da zargin da ake yi wa Iran dangane da alakar da ke tsakaninta da kasar Yemen, inda ta yi la’akari da wadannan tuhume-tuhumen a matsayin maimaita zargin karya da nufin karkatar da hankali daga laifukan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya.
A sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta ce: Wadannan tuhume-tuhume ne da maimaita zarge-zargen karya da ke alakanta matakan gwagwarmaya da al’ummar Yemen suka dauka na kare kansu da kuma goyon bayan al’ummar Falastinu ga Iran. Wannan cin mutunci ne ga al’umma masu yakar zalunci.
Sanarwar ta kara da cewa: Amurka ta hanyar goyon bayan kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya suke yi, ita ce ta shiga yakin da take yi da al’ummar kasar Yemen, kuma tana aikata laifukan yaki ta hanyar kai hare-hare kan ababen more rayuwa da farar hula a garuruwa daban-daban na kasar ta Yamen. Harkar Yemen na goyon bayan Falasdinawa wani mataki ne mai cin gashin kansa, wanda ya samo asali daga zurfin jin kai da kuma fahimtar Musulunci na hadin kai da al’ummar Falasdinu da ke da alhakin wannan mataki na Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Yemen Ta Kakaba Takunkumi Kan Amurka A harkokin Fitar Da Man Fetur Din Kasarta
Kasar Yemen ta haramta fitar da man da Amurka ke fitarwa a matsayin mayar da martani ga wuce gona da irin sojojin Amurka kan kasarta
Cibiyar kula da ayyukan jin kai da ke birnin Sana’a na kasar Yemen ta sanar da dakatar da fitar da mai da Amurka ke fitarwa daga ranar 17 ga watan Mayu, a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen.
Cibiyar daidaita ayyukan jin kai da ke birnin Sana’a ta sanar a safiyar ranar Asabar, matakin hana fitar da danyen mai da Amurka ke yi daga cibiyoyin man fetur na kasar, wanda zai fara aiki daga ranar 17 ga watan Mayun wannan shekara ta 2025.
Wannan shawarar dai ta zo ne a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ke kaiwa kan fararen hula da ababen more rayuwa a Yemen. A cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar ta ce: Kamfanonin da suka karya dokar, za a sanya su cikin jerin wadanda aka kakaba musu takunkumin da aka sanyawa masu ta’addanci kan kasar Yemen.