Aminiya:
2025-08-03@00:09:37 GMT

Wa zai cire wa Real Madrid kitse a wuta?

Published: 4th, May 2025 GMT

Duk da nasarorin da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu a kakar 2023/24 na lashe kofuna 5, ciki har da Kofin Zakarun Turai, amma tana fuskantar ƙalubale a kakar bana, inda ake ganin da wahala ta iya lashe wani kofi bayan Super Cup da ta ci a farkon kaka, da ta ƙwace a hannun Atlanta da ci 2-0 a filin kwallon kafa na National Stadium Warsaw da ke Poland.

Magoya baya na zargin Ancelotti da rusa kungiyar

Magoya bayan Real Madrid da dama sun yi a manna cewa kwai laifin mai horarswa Carlo Ancelotti, duk da tarin nasarori da ya jagornaci kungiyar ta samu a kaka uku da suka wuce, ciki har da lashe Kofin Zakarun Turai 2 da Laliga 2, baya ga wasu kananan kofuna guda hudu — Super Cup guda biyu da King Cup da kuma Club World Cup.

Amma duk da haka wasu magoya bayan kungiyar ba su gamsu da kamun ludayinsa ba a wannan kakar inda suke ganin ba ya ba wa matasa dama su baje basirarsu, ya fi fiifta ’yan wasan da suka fi shahara a kugiyar.

Da wannan ne wasunsu suke gani kamar kocin ya jahilci sabon sauyin da harkar kwallon kafa ta samu na amfani da matasa masu tasowa a sha dayan farko.

Brazil na neman Ancelotti ido rufe

A kwanakin bayan an yi ta rade-radin cewa Real Madrid na kokarin raba gari da Ancelotti, amma dai da har yanzu babu wani rahoto mai karfi da ke tabbatar da hakan.

Amma wasu rahotanni sun ce Ancelotti mai shekarau 65 zai ci gaba da tattaunawa kan karbar aikin horar da tawagar ’yan wasan kasar Brazil kafin watan Yuni, inda zai gana da wakilan Hukumar Kwallon Kafar Brazil (CBF).

Game da batun makomarsa Brazil, Ancelotti dan asalin Italiya, ya ce “za ci gaba da a tattaunawa a makon gobe.”

Ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar bayan da Barcelona ta casa Real Madrid ta lashe Copa del Rey a Sevilla.

Hakazalika, an gani hangi attajirin nan dan kasar Brazil, Diego Fernandes, wanda ke wakiltar Hukumar CBF ya halarci wasan El Clasicon da aka yi a Sevilla, kuma fahimci cewar ziyayar ta Fernandes zuwa Turai, na da alaka da lallashin kocin na Real Madrid ya karbi horas da tawagar CBF da zarar an kammala kakar Sifaniya.

Ke nan idan sun daidaita, akwai yiwuwar Ancelotti zai bar Real Madrid kafin gasar Club World Cup da za a yi a Amurka a bana.

A halin da ake ciki Ancelotti shi ne kan gaba a jerin masu horaswa da Brazil ke fatan dauka, domin maye gurbin Doribal Junior, wanda ta kora bayan da Argentina ta caskara kasar da ci 4-1 a Buenos Aires a watan jiya.

Brazil tana mataki na hudu a teburin Kudancin Amurka a wasannin neman shiga Gasar Kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Kanada da kuma Medico.

Duk da cewa ba ta fuskantar barazarar kasa zuwa babbar gasar ta duniya, Brazil ta ta yi amannar cewar Ancelotti ne kadai zai kai ta ga kara lashe kofin.

Tun kafin a fara Copa America a bara, Brazil take ta zawarcinsa, amma hakarta bai cimma ruwa ba.

Wa zai maye gurbin Ancelloti?

Ana sa ran idan har Real Madrid ta rabu da Ancelotti za ta maye gurbinsa da tsohon dan wasanta na tsakiya, Xabi Alonso, wanda yanzu shi ne kocin Bayer Leverkusen.

Alonso ya yi nasarar lashe Kofin Bundesliga a kakar 2023/2024 a Kungiya Bayer Leverkusen tare da kafa tarihin buga wasa 52 ba tare da an duke su ba, wanda ke ciikin abubuwan da sa yake kamshin turaren dan goma ga kungiyoyi da dama.

Sai dai kuma Xabi ya watsi da duk wani tayi da ke gabansa, yana mai sa ran amsar tayin Real Madrid kadai.

Amma wasu rahotonni sun nuna Real Madrid din tana kwadayin tsohon kocin kuniyar kwallon kafa ta Liverpool dan kasar Jamus, Jurgen Klopp.

Duk da cewa har yanzu ba a ji daga bakin bangarorin biyu ba, amma ga dukkan alamu kungiyar ta fi mayar da hankali a kan tsohon dan wasanta na tsakiya Xabi Alonso.

Raunin ’yan wasa: Madrid ta ji a jikinta

A wannan kakar Madrid ta yi fama da kalubalen samun raunin ’yan wasa, inda tun a farkon kaka ’yan wasan bayanta biyu na sha dayan farkon suka ji mummunar raunuka — Cikinsu har da Mataimakin Kyaftin dinta dan kasar Sifaniya, Dani Carvajal da kuma Eder Militao dan kasar Brazil.

Tuni dai daman David Alaba yana fama da jinya na tsawon lokaci.

Wannan yanayi ya sa kungiyar ta wayi gari ba ta da zabi face ta dinga sirka ’yan wasan baya dana tsakiya a wasannin da ta doka a wannan kakar.

’Yan kwallon Faransa na tsakiya Tchuameni da Camabinga da kuma dan tsakiya Balberde ne yanzu suke bada gudunmawa a baya.

Kalubalen da ke gaban Real Madrid a bana

Real Madrid tana bukatar maki 15 a wasannin da suka rage mata a gasar La Liga a kakar 2024/25.

A halin da ake ciki, Real Madrid mai rike da La Liga na bara tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki hudu tsakaninta da Barcelona da ke saman teburin.

Da ma tuni Arsenal ta yi waje da ita a Gasar Zakarun Turai, yayin da Barcelona ta lashe Spanish Super Cup ta kuma kwace Copa del Rey daga hannunta a kakar nan.

A yau Lahadi, 4 ga watan Mayu za a fafata tsakaninta da Celta a Santiago Bernabeu a wasan mako na 34 a gasar La Liga.

A wasan farko da suka buga watan Oktoban 2024 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu, Barcelona ce ta yi nasarar cin 4-0.

Ranar Lahadi 11 ga watan Mayu za a fafata a wasan hamayya na El Clasico inda kungiyar da Carlo Ancelotti da ke rike da kambu za ta je gidan Barcelona a wasan a mako na 35.

Daga nan za ta fafata a sauran wasannin La Liga uku da za su rage mata, inda za ta karbi bakuncin Mallorca, sannan ta je Sebilla ta karkare da Sociedad a gida.

Bayan kammala wasannin Gasar La Liga na bana, Real za ta buga Club World Cup da za ta fara wasan farko da Al Hilal ranar 18 ga watan Yuni a Amurka.

Wasannin da suka rage mata a bana

Real Madrid – Celta, La Liga mako na 34 (Lahadi 4 ga Mayu). Barcelona – Real Madrid, La Liga mako na 35 (Lahadi 11 ga Mayu). Real Madrid – Mallorca, La Liga mako na 36 (Litinin 14 ga Mayu). Sevilla – Real Madrid, La Liga mako 37 (Alhamis 17 ko 18 ga Mayu). Real Madrid – Sociedad, La Liga mako na 38 (Alhamis 24 ko 25 ga Mayu).

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arsenal Barcelona Carlo Ancelotti Gasar Zakarun Turai kwallon kafa

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere

Kungiyar wasan Taekwondo ta JMI kuma guragu, sun zama zakara a wasan taekwondo gurago sun lashe gasar ta Asia karo na 10 a jere.

Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto cewa an gudanar da gasar ne a kasar Malasiya, kuma yan wasa 107 ne daga kasashe 18 suka sami damar halattar gasar a ranar Jumma’an da ta gabata.

Alireza Bakht da Mamed Haqshenas da kuma Marzieh Nasrollah sun sami lambobin Zinari sannan  Saeed Sadeghianpour, Maryam Abdollahpour, da Amir mohammad Haghitshenas sune suka sami lambobin azurfa.

A yayinda Aylar Jami, Leila Mirzaei, Mohammad Taha Hassanpour, Roza Ebrahimi, Leila Rahimi, da Mehdi Pourrahnama kuma suka sami lamabobin tagulla guda 6.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta yi gargadi game da makircin Isra’ila na kawo cikas ga tsaron yankin August 2, 2025 Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar August 2, 2025 Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi August 2, 2025 ‘Yan Sudan dama na komawa gida bayan gudun hijira na tsawon shekaru a Masar August 2, 2025 Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa August 1, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna August 1, 2025 Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta August 1, 2025 Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 1, 2025 Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama August 1, 2025 Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?
  • Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere
  • Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana
  • Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara
  • Kare Ya Ciji Tsohon Ɗan Wasan Barcelona A Mazakuta