Ƙungiyar mayaƙan ISWAP sun mamaye garin Buni Gari a daren Juma’a da ƙarfe 12:00 na dare, mahaifar Gwamna Buni da ke ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe inda suka kai wani harin ba zata a garin da kuma barikin soja ta 27 da ke garin.
Wata majiya mai tushe daga garin ta tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na daren Juma’a, inda maharan suka ƙona wani ɓangare na hedkwatar rundunar ta 27 da ke Buni Gari a Jihar ta Yobe.
Wannan gari na Buni Gari wadda bai wuce kilomita bakwai ba daga Buni Yadi hedkwatar ƙaramar hukumar ta Gujba wanda ke ɗauke da makarantar sojoji ta musamman kusan yanki ne da maharan ƙungiyoyin ‘yan Boko Haram da ISWAP suka fi kai kawo lokaci zuwa lokaci sakamakon kusancin da wani babban dajin da ya haɗa da dajin Sambisa.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa, lokacin da waɗannan ’yan ta’addan suka iso garin sun yi ta harba makamansu ta kowace kusurwa lura da cewar garin na gaɓar dazuzzukan da ke kewaye da shi kafin daga bisani su shiga wani ɓangare na barikin sojan inda suka ƙona wasu gine-gine na mazauna yankin.
Aminiya ta tattaro rahoton cewa, a halin yanzu jami’an soji da ke ƙarƙashin rundunar Operation Haɗin Kai sun yi artabu da waɗannan ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan ISWAP ne.
Wata majiya mai tushe daga rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar wani takaitaccen bayani da ta fitar a sahfinta na sada zumunta na X ( Twitter) a ranar Asabar.
Sai dai majiyar leƙen asiri na cewar, ’yan ta’addan sun kai hari a garin, inda suka riƙa harbe-harbe, amma cikin gaggawa sojojin tare da haɗin gwiwar mafarauta da ‘yan banga suka shiga tsakani inda suka shawo kan lamarin tare da fatattakar waɗannan ‘yan ta’addan.
Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani ƙarin bayani dangane da harin da kuma ko an yi asarar rayuka a hukumance.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas
A ranar Laraba ne jami’an sojojin ruwa na Najeriya da ke Fatakwal suka ceto fasinjoji 99 daga wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Bukuma da ke ƙaramar hukumar Degema a Jihar Ribas.
Jirgin ruwan, wanda yake na jigilar fasinja yana kan hanyarsa ta daga Fatakwal zuwa Ƙaramar hukumar Akuku-Toru, inda ya yi karo da wani jirgin ruwa a tsakiyar kogin.
Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara Dalilin da ya sa aka samu fashewar abubuwa a barikin Maiduguri – SojojiJami’ar yaɗa labarai na sansanin, Laftanar Kwamanda Bridget Bebia, a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, ta ruwaito Kwamandan sojojin masu aikin bincike, Commodore Cajethan Aniaku, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar Aniaku, ba a samu asarar rai ba, kuma an kuɓutar da akasarin kayayyakin fasinjojin tare da ceto su daga cikin jirgin.
Rundunar sojin ruwan ta ce jami’anta da ke NSS 035 tare da tallafin jiragen ruwa huɗu sun ƙaddamar da aikin bincike mai inganci, inda suka yi nasarar ceto dukkan fasinjoji 99.
“Saboda saurin agajin da tawagar ceto ta yi, ba a sami asarar rayuka ko jikkata ba,” in ji Rundunar Sojan Ruwa.