An Gudanar Da Taron WASA Na Rundunar Sojin Najeriya A Gusau
Published: 26th, January 2025 GMT
Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana wa al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki daya aniyar rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron wasannin rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau.
Taro West African Social Activities WASA wani taro ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin wasannin gargajiya na wannan yankin na Afirka.
Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu cikin annashuwa domin wasannin al’adun da kuma bikin ƙarshen shekara.
Janar Opurum wanda ya jaddada kudirin rundunar na kawar da ‘yan fashi da kuma dawo da zaman lafiya a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba daya, ya yi kira ga sojojin da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, yana mai jaddada cewa, sadaukarwarsu da na da matukar muhimmanci wajen samun zaman lafiya mai dorewa.
Kwamandan Birgediya wanda ake yi wa lakabi da “Jar Kunama”, ya yabawa al’ummar Zamfara bisa yadda suke ba da hadin kai, musamman ta hanyar samar da muhimman bayanan sirri, wanda ya haifar da gagarumar nasara.
Tun da farko, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Meriga ya wakilta, ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa namijin kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar ta Zamfara.
Taron WASA na bana a Gusau ya samu halartar manyan baki da suka hada da sarakunan gargajiya da shugabannin sauran hukumomin tsaro kamar rundunar sojojin saman Najeriya da jami’an tsaro da dai sauransu.
Muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron sun hada da, baje kolin al’adu da raye-raye, wasan kokowa, da dai sauransu.
Yayin da wasu da dama da suka yi nasara suka je gida da kyaututtuka daban-daban da suka hada da man girki, shinkafa da sauran kyaututtuka.
Daga Aminu Dalhatu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A yau, da dama daga cikin matasan Najeriya na fama da matsaloli masu tarin yawa, musamman wajen ciyar da kansu da biyan buƙatunsu na yau da kullum.
Wannan na faruwa ne sakamakon halin da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki, rashin aikin yi, da kuma tsadar rayuwa.
NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da LafiyarmuWasu daga cikin matasan sun kammala karatu, wasu kuma suna da sana’o’in hannu, amma duk da haka, rashin samun aikin da zai biya musu buƙatunsu yana ƙara jefa su cikin mawuyacin hali.
Wannan matsala na ci gaba da haddasa damuwa ga matasan ƙasar, inda da dama daga cikinsu ke fuskantar ƙuncin rayuwa sakamakon rashin tabbas a makomarsu.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana, zai nazarci irin waɗannan ƙalubale da matasa ke fuskanta, musamman a matakin farko na rayuwarsu.
Domin sauke shirin, latsa nan