Manzon Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaba Nguema Na Gabon
Published: 5th, May 2025 GMT
Bisa gayyatar da shugaban kasar Gabon Brice Nguema ya yi, Mu Hong, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, ya halarci bikin rantsuwar kama aiki na shugaba Nguema, a birnin Libreville na Gabon, a ranar Asabar da ta gabata.
Yayin ganawarsu, Mu Hong ya ce kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa tare da kasar Gabon, da daga huldar dake tsakanin kasashen 2 zuwa wani sabon matsayi. A nasa bangare, shugaba Brice Nguema ya ce kasarsa za ta ci gaba da tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kokarin zurfafa hadin kai tare da kasar Sin a bangarori daban daban. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.