Sojojin HKI Sun Rushe Gidajen Falasdinawa Fiye Da 100 A Yammacin Kogin Jordan
Published: 5th, May 2025 GMT
A cikin wata daya kadai sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 152 a yammacin Kogin Jordan.
Majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa a kudancin garin Khalil ‘yan mamayar sun rushe gidaje 25 da kuma wasu cibiyoyi, da hakan ya sa adadin gidajen da su ka rushe zuwa 152 kamar yadda hukumar Falasdinu ta ambata.
Bugu da kari, majiyar Falasdinawan ta ce, ‘yan mamayar sun kuma aike wa da wasu cibiyoyin da gidaje 46 gargadin cewa za su rushe su, da yin kira da su fice daga cikinsu.
Wata cibiyar ta Falasdinawa ta ce fada wa kamfanin dillancin labarun “Anatoli’ cewa; ;yan mamayar sun rushe gidaje 96 da mutane suke rayuwa a cikinsu, sai kuma wasu gidaje 10 da babu mutane a ciki.Haka nan kuma rusau din ya shafi wasu cibiyoyin noma 34.
Mafi yawancin gidajen da aka rushe dai suna a yankin Tubas ne, Khalil sannan kuma da birnin Kudus.
Wani rahoto ya ambaci cewa; A cikin watan da ya gabata,’yan mamaya suna nazarin gina matsugunan ‘ya share wuri zauna 27 a cikin birnin Kudus.
A gefe daya, ‘yan share wuri zauna din sun kai hare-hare akan Falasdinawa har sau 1693 wanda ya fara a cikin watan Afrilu. Hare-haren kuwa sun hada lalata hanyoyi da tunbuke bishiyoyi, a kwace filayen Falasdinawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina ta kori ɗalibanta 57 kan laifin satar jarabawa.
Hukumar gudanarwar jami’ar ta kuma dakatar da wasu dalibai biyar na tsawon shekara guda tare da ba wasu biyu takardar gargaɗi kan aikata laifukan jarabawa.
A safiyar Asabar kakakin jami’ar, Hajiya Fatima Sanda, ta sanar da cewa majalisar jami’ar ta amince da matakin ne bayan karɓar rahoton kwamitin ladabtarwa kan laifukan jarabawa na jami’ar.
Sanarwar ta ƙara da cewa an dakatar da ɗalibai biyar na tsawon shekarar karatu biyu, tare da soke duk jarabawarsu da laifin ya shafa.
Jami’ar ta kuma jaddada cewa ba za ta lamunci aikata laifukan jarabawa ko rashin ɗa’a ba.