Trump Na Shan Suka Kan Wallafa Hotonsa Na AI Sanye Da Kayan Fafaroma
Published: 4th, May 2025 GMT
Shugaban Amurka, Donald Trump na shan suka daga wasu jagororin mabiya ɗarikar Katolika, saboda wallafa hotonsa da ya samo daga manhajar ƙirƙirarriyar basira ta AI, sanye da kayan fafaroma.
Mista Trump ya wallafa hoton ne a shafukan sada zumunta na fadar White House.
Matakin na zuwa ne yayin da mabiyar ɗarikar Katolika, ke shirin zaɓen sabon fafaroma, bayan alhinin da suke ciki na rasuwar jagoran ɗarikar, Fafaroma Francis, wanda ya mutu ranar 21 ga watan Afrilu.
Taron mabiya ɗarikar Katorlika na birnin New York ya zargi Shugaba Trump da zolayar Addininsu.
Wallafa hoton na zuwa ne kwanaki bayan da shugaban ya zolayi wani mai bayar da rahotonni da cewa ”ina son zama fafaroma”
Ba Trump ne shugaban Amurka na farko da aka taɓa zarga da zolayar mabiya ɗariƙar Katolika ba.
A shekarar da ta gabata ma an zargi tsohon shugaban Amurka, Joe Biden lokacin da ya sanya hannu kan alamar kuros a lokacin wani gangamin masu goyon bayan zubar da cikin a Tampa da ke jihar Florida
A ranar Laraba mai zuwa ne fadar Vatican za ta fara shirye-shiryen zaɓen sabon fafaroma.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Fafaroma
এছাড়াও পড়ুন:
An rantsar da Brice Nguema a matsayin shugaban Gabon
An rantsar da mista Brice Nguema a matsayin shugaban kasar Gabon, a birnin Libreville fadar mulkin kasar
Shugabannin kasashen Senegal, da Equatorial Guinea, da Rwanda, da dai sauransu na dag cikin bakin da suka halarci bikin.
An ce, bikin rantuwar kama aiki na wannan karo shi ne irinsa na farko a kasar Gabon mai bude kofa ga jama’ar kasar, don haka aka samu kimanin mutane 40,000 da suka je kallon bikin.
Kafin hakan an rantsar da Brice Nguema bayan ya lashe babban zaben kasar da ya gudana a shekarar nan ta 2025, inda ya yi nasarar lashe kaso 94.85% na jimillar kuri’un da aka kada.