Saudiyya Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Aikin Hajji Babu Takardun Izini
Published: 6th, May 2025 GMT
Wanda ya ba su masauki a otal, gida, ko wani wurin zama shi ma zai fuskanci irin wannan hukunci.
Duk wanda ya je aikin Hajji ba tare da izini ba ko dan ƙasa ne ko wanda ya daɗe fiye da lokacin zama za a kori mutum zuwa ƙasarsa tare da dakatar da shi daga shiga Saudiyya na tsawon shekaru 10.
Hukumomin shari’a za su kuma karɓi motocin da aka yi amfani da su wajen safarar waɗanda ba su da izinin yin aikin Hajji, musamman idan motocin na masu laifin ne.
A wani labari da ya shafi aikin Hajji, Hukumar Hajji ta Ka6sa (NAHCON) ta sanar da cewa jigilar mahajjatan Nijeriya na shekarar 2025 zai fara ne daga ranar 9 ga watan Mayu.
A cewar wata sanarwa da Daraktar Watsa Labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar ta ce mahajjata 43,000 ne suka riga suka biya kuɗin Hajji a bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe
Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum shida bisa zargin tono gawar wani mutum a kabari tare da cire sassan jikinta domin yin asiri.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Kawuji Sarki, mai shekaru 39, ya amsa laifin.
Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma RibasYa bayyana cewa wani mutum mai suna Aliyu Chindo ne, ya ba su aikin cire idanun mamacin, tare da yi wa kowannensu alƙawarin Naira 500,000.
Sai dai ya ce bayan kai masa sassan jikin, Chindo ya gudu ba tare da ya biya su ba.
Nan take jami’an tsaro suka cafke su.
An gano cewa sun tono kabarin wani tsoho mai shekaru 85, Mallam Manu Wanzam, wanda aka binne a ranar 9 ga watan Satumba a maƙabartar Gadam Arewa da ke Ƙaramar Hukumar Kwami.
Kakakin NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya bayyana sunayen sauran da aka kama: Adamu Umar (22), Umar Jibrin Aboki (21), Abdullahi Umar Dauda (17), Muhammed Isa Chindo (28), da Manu Sale (23).
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da neman Aliyu Chindo da ya tsere.
Kwamandan hukumar a jihar, Jibrin Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “rashin imani,” tare da tabbatar da cewa za su gurfanar da waɗanda suka kama a kotu bayan kammala bincike.