Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma
Published: 27th, March 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu.
Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar.
Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan NajeriyaƘudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar.
Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin bayan cece-kucen da hakan ya haifar a faɗin ƙasar.
Ƙudurorin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke nazari a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.
Aminiya ta ruwaito cewa, majalisar ta janye ƙudirin ne bayan gwamnatocin jihohin sun bayyana adawarsu kan matakin da ke neman tuɓe musu rigar alfarmar da ke bai wa gwamnoni da mataimakansu da kuma mataimakin shugaban ƙasa kariya daga fuskantar tuhuma kan laifuka.
A ranar Larabar da ta gabata ce ƙudirin ya samu karatu na biyu a zauren majalisar, ƙarkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Gwamnatin Iran Ta Ce daga Yau Lahadi Wuraren Fakewa A Bude Suke Sa’o’I 24 A Tehran
Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa, kasar Iran ta shiga yaki, kuma don haka dole sai an sami sauyi a rayuwar mutane ba. Fatima Muhajirani ta bayyana cewa daga yau ramukan layin dogo a cikin birnin Tehran wuraren mafaka da muyewa ne na mutanen da suke birnin har’ila yau za’a bude masallatai da makarantu don su zama wuraren samun mafaka.
A wani bangare fatimeh Muhajirani ta bayyana cewa an rufe sararin samaniyar kasar Iran, don haka babu jirgi wanda zai tashi a ciki ko wajen kasar har zuwa abinda hali yayi ta kuma kara da cewa a halin yanzu jirgin kasa zai zama hanyarb tafiya mafi sauki a wannan haling a mutane. Tace mahajjan Iran zasu dawo ta hanya daga kasar Iraki bayan sun yada zango a birnin Najaf na kasar Irakin.
Sannan ta bayyana cewa abinci da makamashi da magunguna a asbitoci da dakunan shan magani suna nan isassu a kasar. Amma ta sake nanatawa.