Matashi ya kashe mahaifinsa da adda a Jigawa
Published: 6th, May 2025 GMT
Wani matashi dan shekarar 20 ya fada hannun hukuma kan zargin kashe mahaifinsa da adda a Jihar Jigawa.
Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wanda ake zargin kashe mahaifinsa mai shekara 57, da adda.
Wanda aka kashe ya samu raunuka a kafadarsa da wuya da kirjinsa, kuma an kai shi Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin 5 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 10:00 na safe a unguwar Bakin Kasuwa, da ke Karamar hukumar Gwaram.
Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano ’Yan PDP 6 a Majalisar Tarayya sun koma APC Daukar nauyin dalibai: Rikici ya barke a Hukumar Raya Arewa Maso YammaKwamishinan ’yan sandan Jihar Jigawa, AT Abdullahi, ya ba da umarnin cewa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) da ke Dutse su karɓi ke cin domin don gudanar da bincike mai zurfi, wanda bayan nan za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuga.
Kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da kama wanda ake zargin tare da ba da tabbacin cewa za a yi adalci kuma za a bayar da ƙarin bayani a nan gaba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi
Aƙalla mutane 58 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon barkewar cutar Kwalara a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 da ke jihar Bauchi.
Haka kuma, an samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar a faɗin jihar.
Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar ratayaMataimakin Gwamnan jihar, Auwal Mohammed Jatau, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wasu kwamitoci biyu kan yaki da cutar a jihar.
Mataimakin Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda barkewar cutar ke ci gaba da kashe mutane, lalata rayuwar jama’a, da kuma jefa tsarin kiwon lafiya na jihar cikin matsala.
Jatau ya bayyana cewa: “Ana iya kaucewa wannan barkewar cutar idan aka ɗauki matakan gaggawa, aka haɗa kai wajen tunkarar cutar, tare da ci gaba da inganta ruwa, tsafta da kula da muhalli. Jihar Bauchi ta samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar, tare da mutuwar wasu 58.”
Ya ƙara da cewa duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi, Kwalara na ci gaba da zama barazana ga lafiyar jama’a.
Ya ce kafa kwamitin yaki da cutar ba wai kawai ya zo a kan lokaci ba, har ma yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma burin da aka sa gaba na dakile ci gaba da yaduwarta.
A cewarsa: “Wannan kwamitin zai zama ja-gaba wajen jagorancin hukumomin gwamnati a jihar Bauchi kan barkewar Kwalara, tare da tsara dabarun kariya na dogon lokaci da suka yi daidai da Tsarin Ƙasa na Yaki da Cholera da kuma manufofin Cibiyar Dakile Cututtuka ta Najeriya (NCDC).”
Mataimakin gwamnan ya tunatar da mambobin kwamitocin cewa zaɓensu ya nuna ƙwarewarsu, sadaukarwarsu da muhimmancin rawar da za su taka wajen nasarar aikin, tare da fatan za su tabbatar da sa ido, gano cuta da wuri, da kuma ɗaukar matakin gaggawa idan ta barke.