Aminiya:
2025-05-06@19:03:29 GMT

Yadda wani ya mayar da gadonsa motar hawa a Indiya

Published: 6th, May 2025 GMT

A bidiyon da wani mai suna Nawab Sheikh ya fitar na nuna yadda ya hau motarsa, wacce yake tuka ta a kan titunan birnin Murshidabad a cikin ƙasar Indiya, don nishaɗantar da mahaya babur, wanda ya sa bidiyon yake ta yaɗuwa a shafin sada zumunta na Instagram.

Babu wani wuri mafi kyawun nuna bajintar kirkira don jan hankalin ɗan Adam kamar intanet.

Matashi ya kashe mahaifinsa da adda a Jigawa ’Yan PDP 6 a Majalisar Tarayya sun koma APC

Haka kuma idan aka zo fannin ƙirƙirar sabuwar fasaha, ba da yawa ba ne ke irin wannan a cikin Indiyawa.

Na baya-bayan nan shi ne ƙirƙirar da wani mutumin West Bengal – “motar gado” inda ya mai da gadonsa ya koma mota kuma yake tuka ta.

Bidiyon Nawab Sheikh a motar da yake yawo a kan titunan Murshidabad don nishaɗantar da mahaya babur yana yaɗuwa a shafukan Instagram.

Bidiyon ya nuna wani gado da aka mayar zuwa motar tafi da gidanka, mai taya hudu da birki.

Direban motar ne ke sarrafa ta kuma ana sarrafa ta, ta tsarin tuki da sitiyari.

Bayan saka katifa da zanin gado da matashin kai, gadon yana da ƙarin ƙirƙira ta musamman: wanda akwai madubin gefe da ke manne da kowane gefe don taimakon direban kallon bayansa.

Masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani sun yi ta tururuwa wajen yin sharhi, inda suka tofa albarkacin bakinsu a kan wannan kirkira ta musamman.

Wani mai amfani da shafukan ya rubuta, “Indiya ba ta ’yan koyo ba ce.”

Wani mai amfani da shafukan na biyu ya yi dariya, sannan kuma ya aika da alamar dariya.

“Ana iya ganin irin wannan ne a Indiya kawai,” in ji na uku.

Wani mai amfani da manhajar sada zumunta ta X, kodayake ya yi suka kuma ya rubuta, “Shin yana da takardun da ake bukata da amincewa daga sashen hukuma don tuka irin wannan abin hawa a kan hanya?

“Mutane sukan yi watsi da ka’idojin tuki, kawai don son rai.”

“Idan wannan motar ta Nawab ta haifar da wasu hadura fa? Dokokin zirgazirga sun yarda da haka? Ko kuma irin wannan motar ce ake yin gwaji?” wani ya tambaya.

A cewar jaridar Times of India, Mista Sheikh ya kwashe sama da shekara guda yana zuba jarin Naira miliyan 3 don ƙirƙirar wannan motar sannan ya wallafa a dandalin sada zumunta.

Duk da samun karɓuwa da yawa na tukin motar gado a kan tituna, ’yan sanda sun ja motar da ke kan gadon, har ma suka tarwatsa ta saboda matsalar cunkoson ababen hawa a hanyar Jihar Raninagar Domkal.

Sai dai a baya can, akwai wani mutumin Delhi da ya taba canza mota ƙirar Maruti Suzuki Jimny zuwa gado.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Indiya irin wannan

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Mayar Da Martani Akan Zarginta Dangane Da Yemen

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen.

 A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta fitar ta bayyana cewa: Abinda mutanen Yemen suke yi domin taimakawa al’ummar Falasdinu, mataki ne na kashin kansu da su ka dauka cikin ‘yanci saboda lamirinsu na ‘yan adamtaka da kuma taimako na musulunci ga ‘yan’uwansu Falasdinawa.”

Bayanin ya kuma ci gaba da cewa; Jinginawa jamhuriyar musulunci ta Iran abinda mutanen na Yemen suke yi, ba shi da tushe, kuma manufar hakan ita ce, rufe laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi a Falasdinu.”

Bayanin ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci tana sake jaddada matsayarta akan wajabcin kiyaye da karrama kasashe da kasantuwarsu a dunkule a wuri daya, kamar kuma yadda muke yin tir da hare-haren sojan Amurka akan Yemen, domin hakan take dokokin MDD ne, da kuma dokokin kasa da kasa.”

Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira da a kawo karshen kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa da shi ne tuhsen rashin zaman lafiya a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.

Wani sashe na bayanin na ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran din ya ce; al’ummar Iran a shirye suke, su kare kansu daga duk wata barazana akan manufofin kasa, kuma alhakin duk abinda zai faru yana wuyan hukumomin ‘yan ta’adda na Amurka da sahayoniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
  • Iran Ta Mayar Da Martani Akan Zarginta Dangane Da Yemen
  • An Kama Wani Ɗan Ghana Bisa Zargin Kai Mata Hajji Ba Tare Da Lasisi Ba
  • Kasar Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wani Hari Da Zata Fuskanta Daga Makiya
  • Wani harin makami mai linzami daga Yemen ya fada filin jirgin saman Ben Gurion na Isra’ila
  • Iran : Araghchi zai ziyarci Pakistan da Indiya
  • Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu
  • Iran Ta Yaba Da Sadaukarwar Da ‘Yan Jarida Suka Bayar Kan Watsa Wahalhalun Falasdinawa
  • Adadin Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Aiki Da Lantarki Na Sin Ya Karu Da 47.6% A Shekara