Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga 3, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace
Published: 5th, May 2025 GMT
Ƴansandan sun yi nasarar kai hari kan sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Benue da Delta, inda suka kashe mutane uku, suka ceto waɗanda aka sace biyu, tare da kama wasu tara. A Benue, waɗanda ake zargi da shirya hare-hare kan jami’an tsaro sun samu raunuka masu tsanani bayan wata musayar wuta da kusa da Tse-Gondo, inda aka kwato bindigogi biyu da ƙirar gida da wasu harsasai.
A Delta, Ƴansandan sun kama Henry Okpor da ake zargi da sace motoci a ranar 22 ga Afrilu, inda suka kwato bindiga ɗaya da motoci biyu. Kwanaki uku bayan haka, wata tawaga ta musamman ta kama wasu ‘yan daba biyu na ƙungiyar Vikings, inda suka kwato bindigogi biyu da harsasai biyar.
CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20 Gwamnan California: California Za Ta Ci Gaba Da Bude Kofa Ga Sin Domin Gudanar Da KasuwanciAn yi bata kashi a wani iftila’in garkuwa da mutane a Agbarho lokacin da ‘yan sanda suka ceto waɗanda aka sace biyu bayan wata gwagwarmaya a dajin Uvwiama na Ughelli ta Arewa. An kama mutane tara a wannan artabun, tare da kwato bindigogi da dama.
Kakakin ‘yansanda ACP Olumuyiwa Adejobi ya yaba da jajircewar jami’an tsaro, yana mai cewa nasarorin da aka samu sun nuna irin gudunmawar da ‘yansandan Nijeriya ke bayarwa wajen yaki da laifuka a faɗin ƙasar. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da rahoton duk wani abin da zai iya taimakawa wajen warware matsalolin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara
A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara.
A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da fasinjoji ta faɗa cikin gadar da ta ruguje. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SRC Isah Aliyu, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar.
Kwamandan FRSC na jihar, CC Aliyu Magaji, wanda ya ziyarci wurin hatsarin, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa da asarar rayukan, inda mafi yawansu mata ne. Ya ce hatsarin ya biyo bayan nauyin da aka ɗora wa motar fiye da ƙima da kuma tafiya da daddare.
Hukumar ta gode wa mazauna yankin da suka gaggauta taimakawa wajen ceto wasu daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su. Kwamanda Aliyu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Zamfara da al’ummar Gummi, tare da yin kira ga direbobi su rika bin ƙa’idojin hanya da kuma guje wa tuƙa mota da dare domin kare rayuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp