Aminiya:
2025-08-04@13:41:16 GMT

’Yan fashi sun kashe magidanci a Kano

Published: 5th, May 2025 GMT

Ana fargabar cewa wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun kashe wani magidanci a  unguwar Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Bayanai sun ce waɗanda ake zargin sun kashe magidancin ne da adda, bayan sun shiga gidansa da yake zaune domin sata da asuba.

To sai dai mazauna unguwar sun bayyana wa Aminiya cewa sun samu nasarar kama wanda suke zargin shugaban ’yan fashin ne, sun kuma miƙa shi ofishin ’yan sanda na Ɗorayi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan fashi Jihar Kano

এছাড়াও পড়ুন:

Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da babban shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar a shekarar 2025.

An fara dashen ne yankin Yanbawa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda.

Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai  Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi

Gwamnan ya ce wannan shiri na nufin yaƙi da sauyin yanayi, farfaɗo da ƙasar da ta lalace, da kuma kare muhalli.

Ya ce an fara dashen bishiyoyin a wannan fili tun shekarar 1972, amma aka bari ya lalace.

Yanzu gwamnatinsa ta gyara shi don ya taimaka wajen shawo kan matsalolin fari da sauyin yanayi.

Ya ƙara da cewa wannan shiri yana daga cikin ayyukan muhalli da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekara guda.

Ayyukan sun haɗa da gyaran gonakin dasa itatuwa a Garun Malam da Garko, waɗanda yanzu suke samar da dubban ƙananan itatuwa da ake rabawa a Kananan Hukumomin 44 na jihar.

Ya ce tuni aka farfaɗo da sama da hekta 200,000 na ƙasa da ta lalace.

Hakazalika, ya ce an samar da wata gona mai hekta 100 domin koya wa manoma dabarun noman itatuwa da kayan gona.

Gwamnan, ya bayyana cewa suna haɗin gwiwa da Ƙungiyar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), don koyar da yadda ake amfani da ƙasa yadda ya kamata da kula da muhalli.

Ya ce sun kuma fara shirye-shiryen ilmantar da makarantu da al’umma game da sauyin yanayi da muhimmancin kula da muhalli.

Don ɗorewar wannan shiri, gwamnan ya ce an kafa dokar sauyin yanayi da tsarin aiki a Jihar Kano, wanda ya sanya mata hannu.

Haka kuma an kafa ɗakin gwajin gurɓacewar iska da ruwa a Jami’ar Northwest don binciken muhalli.

Ya ce yanzu haka suna fitar da rahotannin lafiyar iska da ruwa a kowane mako daga sabon ɗakin binciken.

Wannan ya nuna cewa gwamnatin tana amfani da kimiyya da bayanai wajen yaƙi da sauyin yanayi.

Gwamnatin ta sake ɗaukar masu tsaron daji, tare da biyansu albashi, sannan ta ɗauki sabbin ma’aikata don kare dazuka a faɗin jihar.

“Dukkanin itacen da muka dasa dole ne ya girma,” in ji gwamnan.

“Shi ya sa muke gina ƙwararrun cibiyoyi da tsarin lura da yadda shirin ke tafiya.”

Za a raba itatuwan a makarantu, wuraren ibada, gonaki, gidaje, wuraren jama’a, da kuma gefen tituna a cikin gari da karkara.

Gwamnan, ya umarci shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 su ɗauki shirin da muhimmanci, su tabbatar da gaskiya wajen raba itatuwan.

“Yanzu ne lokacin da ya dace mu dakatar da yaɗuwar hamada, mu yaƙi sauyin yanayi, da hana zaizayar ƙasa.

“Mu daina sare itatuwa ba tare da tunani ba. Kowa ya dasa, ya kula, kuma ya kare itatuwa don kare ƙasarmu da makomar ’ya’yanmu,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya, matasa, ƙungiyoyi, makarantu da kasuwanni su haɗa kai wajen samar da kyakkyawan muhalli a Kano.

“A yau ne muka ɗauki alhakin gyara ƙasarmu. Allah Ya taimake mu a wannan aikin alheri,” a cewarsa.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Muhammad Dahiru Hashim, ya ce wannan shiri na dasa itatuwa ya nuna irin jajircewar Gwamnan wajen kare muhalli.

Ya bayyana cewa shekara guda da ta wuce, suka fara shirin dasa itatuwa miliyan uku.

Wannan sabon shirin ya ƙara faɗaɗa, kuma an yi amfani da itatuwan da aka noma a cikin jihar.

Ya ce an sake farfaɗo da gonakin gwamnati da ke Gwale da Gwarzo, waɗanda yanzu ke samar da itatuwa don ɗorewar wannan shiri.

Ya ƙara da cewa tun da farko Gwamna Abba, ya nuna irin ƙwarewarsa wajen kare muhalli.

Aikin farko da ya halarta bayan ya hau mulki shi ne bikin Ranar Muhalli ta Duniya ta 2023, wanda ya nuna wa jama’a cewa gwamnatinsa na ɗaukar sauyin yanayi da muhimmanci.

“Jihar Kano ba kawai tana dasa itatuwa ba ne. Muna gyara muhalli, muna tsaftace iska, kuma muna dakatar da yaɗuwar hamada.

“Wannan shiri yana nuna sauyi, da kuma makomarmu,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa ma’aikatan ma’aikatar muhalli, shugabannin gargajiya, saboda irin goyon bayan da suka bayar don nasarar wannan shiri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara
  • Kashe N712bn Kan Gyaran Filin Jiragen Saman Legas Rashin Sanin Ya Kamata Ne – ADC 
  • An kama dilallan ƙwaya 28 a cikin barikin sojoji a Kaduna
  • Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5
  • An Sake Kashe Wata Ɗalibar Jami’ar Ondo
  • Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa
  • Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa
  • Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine
  • PDP ta mutu murus a Kano — Shugaban NNPP
  • NBRDA Za Ta Hada Gwiwa Da KIRCT Domin Habaka Magunguna Da Yaki Da Cututtuka