Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Wutar Lantarki Da Za Ta Raba Wa Jihohi 3 Wuta
Published: 6th, May 2025 GMT
Da yake karin haske game da abubuwan da aka tsara da kuma yadda hukumar za ta kasance, shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Husseini ya shaidawa manema labarai cewa, sanya hannu kan dokar za ta kara samar da damarmakin wutar lantarki a jihohin uku.
Husseini ya jaddada cewa, za ta kuma rage wahalhalu da kuma rage tsadar makamashi ga ‘yan jihohin, za ta kuma samar wa kananan masana’antu da manyan masana’antu isasshen makamashi don yin kasuwanci, tare da bai wa asibitoci da cibiyoyin kula da ruwa damar gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
Dangane da tsarin shugabancin hukumar da ake son yi, Husseini ya ce, za a samar da shugaba, manajan darakta da mataimakin manajan darakta wanda kowace jiha za ta samar da wakilai uku.
Ya kara da cewa, shugaban hukumar zai yi aiki na tsawon shekaru hudu wanda za a rika jujjuyawa a tsakanin jihohin da ke cikin tsarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Karamar Hukumar Bubura Ta Kai Tallafin Kayayyakin Abinci Cibiyar Gyaran Hali
Daga Usman Mohammed Zaria
Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar.
Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya kai ziyara ta duba cibiyar a baya.
A cewarsa, manufar bayar da tallafin ita ce don tallafa musu wajen kyautata rayuwarsu da kuma karfafa musu gwiwa su zama mutane nagari bayan sun fito daga gidan gyaran hali.
A nasa jawabin, jami’in da ke kula da cibiyar gyaran hali ta Babura, ASP Muhammad Ali, ya gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan karamci, yana mai cewa taimakon ya zo ne a lokacin da ake matuƙar buƙata.
A yayin hudubarsa ga fursunonin, Babban Limamin Babura, Imam Salisu Aliyu, ya shawarce su da su nemi gafarar Allah, su kuma kara kusanci gare Shi, tare da rungumar canji mai kyau.
Kayan tallafin da aka bayar sun haɗa da buhunan masara, gero, shinkafa, garin rogo, man gyada, sinadaran dandano, gidan sauro da maganin kwari.
Manyan baƙin da suka raka shugaban ƙaramar hukumar a lokacin ziyarar sun haɗa da Hakimin Babura, Sarkin Bai Ringim, Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha, jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin, CSP Abdu Jinjiri, da jami’in Hukumar Tsaro ta Civil Defence, CSC Sunusi Usman Chamo, da sauransu.