Mahukunta Gandun Daji Na Hadejia Sun Kai Ziyarar Aiki Hukumar NOA
Published: 26th, January 2025 GMT
Hukumar kula da gandun daji na Hadejia ta ce wuraren shakatawa na kasa suna taka rawar gani ta fuskar kiyaye halittu, da magance matsalolin sauyin yanayi, da inganta bincike, da ci gaba, gami da samar da ayyukan yi a Najeriya.
Mukaddashin jami’in kula da gandun dajin, Mista Jonah Moses ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar neman shawarwari ofishin wayar da kan jama’a na kasa da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Ya nanata cewa al’umma za su kara fahimtar fa’idojin irin wadannan wurare ne kadai idan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa NOA, ta taimaka wajen fadakarwa ko ilmantar da jama’a.
Jonah Moses ya bayyana cewa, sun kawo ziyarar ce domin ganawa da masu ruwa da tsaki irin su hukumar ta NOA, wadanda za su iya taimakawa wajen fahimtar da jama’a game da gandun daji na Hadejia.
Da yake mayar da martani, Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jma’a ta kasa NOA na jihar Jigawa, Malam Ahmad Tijjani Ibrahim ya yabawa mai kula da gandun dajin na Hadejia da tawagarsa bisa da kwazon da suke nuna wajen tafiyar da ayyukansu.
Ya kara da cewa hukumar ta ba da fifiko kan batun sauyin yanayi, inda ta samar da sashen kula da muhalli, da yanayi, da makamashi.
Shugaban hukumar ta NOA ya tabbatar wa tawagar cewa a shirye hukumar ta ke na zaburar da al’ummar kasa game da ayyukan gandun dajin.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumomin Ilimi a Jihar Jigawa Sun Kare Kasafin Kudinsu a Gaban Majalisa
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar bunkasa ilimin manya ta jihar Jigawa tace za ta kashe naira milyan 400 wajen gudanar da harkokin ta a sabuwar shekara ta 2026.
Shugaban hukumar. Dr. Abbas Abubakar Abbas, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin hukumar a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Dr Abbas Abubakar Abbas ya ce hukumar za ta yi amfani da kudaden wajen inganta shirye shiryen koyon karatu da rubutu ga manya maza da mata da na ci gaba da karatu don kammala karatun sakandare da na masu son sake jarrabawar sakandire da koyon karatu ta Rediyo da cibiyoyi daban daban da ke fadin jihar.
Shi ma da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumarsa , shugaban hukumar makarantun Tsangaya, Dr. Hamisu Maje, ya ce sun yi kiyasin naira milyan dubu 3 da milyan 500 tare da kudurin kammala aikin ginin makarantun Tsangaya guda 3 da ke Ringim da Kafin Hausa da Dutse.
Ya ce an yi tanadi domin kafa cibiyar koyar da sana’oi da gidajen alarammomi da masallaci tare da samar da ruwan sha da wutar lantarki a kowacce makaranta.
Dr. Hamisu Maje ya kuma bayyana cewar hukumar za ta gyara makarantun Tsangaya guda 7 da aka gada daga gwamnatin tarayya da ke sashen jihar domin karfafa tsarin ilimin makarantun Tsangaya na zamani.
A daya bangaren kuma, kwalejin fasaha ta jihar da ke Dutse da Kuma hukumar bada tallafin karatu ta jihar sun kare kiyasin kasafin kudadensu a gaban kwamatin kula da manyan makarantu na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Da ya ke kare kiyasin kasafin kudin, shugaban kwalejin fasaha ta jihar da ke Dutse, Dr. Ahmad Badayi, ya ce sun yi kiyasin fiye da naira milyan 700 wadda daga ciki an kebe naira milyan 330 domin sayo kayayyakin aiki a dakin gwaje-gwaje da koyon aikin hannu da gyaran ofisoshi, yayin da za a yi amfani da ragowar kudaden wajen kammala manyan ayyuka.
Shi ma da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumar sa, shugaban hukumar bada tallafin karatu ta jihar Malam Sa’idu Magaji, ya ce sun yi kiyasin kashe naira milyan dubu 10 domin bada tallafin karatu na cikin gida da na kasashen waje.
A nasa jawabin, shugaban kwamatin kula da ilimin manyan makarantu na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Sule Tankarkar Alhaji Muhammad Abubakar Sa’id, ya jaddada bukatar ganin masu ruwa da tsaki a bangaren manyan makarantu sun yi dukkan mai yiwuwa domin inganta harkokin ilimi mai zurfi a sabuwar shekara.