Kafar United Daya Ta Kai Wasan Karshe A Gasar Europa League
Published: 4th, May 2025 GMT
Ƙafar Manchester United guda ta kai wasan ƙarashe na gasar Zakarun Turai ta Europa League bayan da ta doke Athletic Bilbao da ci 3-0 a Sifaniya.
Da fari wasan ya nuna kamar ba zai yi wa United kyau ba, to amma bayan minta 30 sai wasan ya sauya bayan da Harry Maguire ya yi wata bajinta tare da buga ƙwallo zuwa da’irar bilbao, lamarin da ya bai wa Casemiro damar zura ƙwallon farko a wasan.
Minti uku bayan nan ne United ta ƙara samun wata damar bayan da ɗan wasan bayan Bilbao, Dani Vivian ya yi wa Rasmus Hojlund ƙeta a yadi na 18, inda bayan duba na’urar taimaka wa alƙalin wasa ta VAR, aka bai wa Vivian jan kati tare da bai wa United bugun fenareti.
Bayan da Bruno ya buga fenaretin ya kuma ci, ya ƙara ta uku kafin tafiya hutun rabin lokaci bayan da ɗan wasan Bilbao ya yi kuskure.
A mako mai zuwa ne United – wadda kofin Europa ne kawai fatanta a wannan kaka – za ta karɓi baƙunci Bilbao a filin wasa na Old Trafford.
A ɗaya wasan na Europa kuwa, Tottenham ce ta samu nasara kan Bodø/Glimt da ci 3-1 a Ingila.
Masu nazarin ƙwallon ƙafa na hasashen buga wasan ƙarshe tsakanin ƙungiyoyin Ingila, United ta Tottenham a gasar ta Europa, wani abu da aka jima ba a gani ba.
Can ma a ƙaramar gasar ta Conference League, Chelsea ta samu nasarar doke Djurgården da ci 4-1, wadda ita ma ake hasashen za ta kai wasan ƙarshe na gasar.
A mako mai zuwa ne Arsenal za ta je gidan PSG a babbar gasar Zakatun Turai ta Champions League, da nufin ɗaukar fansa kan ci 1-0 da PSG ta yi mata a Emirates.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Wasanni
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar NPA Ta Ce Za A Kammala Aikin NSWP A Zango Na Daya A 2026
Cibiyar samar da kyakyawan yanayin yin kasuwanci na Fadar Shugaban Kasa da hadaka da NPA ne, suka shirya taron kaddamarwar,
“Ana sa ran a zangon farko na 2026, aikin na NSWP zai fara fara aiki wanda tuni, Fadar Shugaban Kasa ta amince da kwangilar domin a wanzar da aikin,” Inji Dantsoho.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa, za a rinka gudanar da ganawa akai-akai da masu ruwa da tsaki domin gudanar da hada-hadar kasuwanci a cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar a cikin nasara.
Ya sanar da cewa, zuba hannun jari a kayan aiki Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, samar da kayan aiki na fasahar zamani da sauransu, za su taimaka wajen kara habaka kasa da kuma gudanar da ayyuka, a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
Dantsoho ya kara da cewa, kayan aikin da ke a musamman Tashoshin Jiragen Ruwa na Apapa da Tin Can Island, sun jima ana yin amfani da su a kasar nan, wadanda kuma akwai bukatar a yi masu garanbawul.
“Yau kimanin shekaru 48 ke nan, da kafa Tashar Jirgin Ruwa ta Tin Can Island, inda kuma ta Apapa ta kai kimanin shekaru 100, amma har yanzu, ba a yi masu wani garanbawul ba,” A cewar Dantsoho.
Sai dai, ya sanar da cewa, amincewar kwanan baya da Gwamnatin Tarayya ta yi na a yiwa daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar garanbawul, hakan zai kara taimakawa wajen gudanar da ayyuka a Tashoshin.
A bangaren kimiyya Shugaban ya bayyana cewa, Hukumar na ci gaba da aiki kafada da kafada da kungiyar kula da harkokin teku ta kasa da kasa wato IMO, domin yin amfani da tsarin PCS, duba da cewa, inda ya alakanta aikin na NSWP, a matsayin wani banban ginshiki.
Dantsoho ya jadda cewa, tsarin na PCS, zai kawar da yin amfani da takardu, da kuma yin shisshigi, wanda hakan zai kuma kara tabbatar da kawar da duk wata badakala da za ta iya kunno kai da rage tsada da kuma kara samar da kudaden shiga.
“Hukumar ta NPA kadai, ba za ta yi cimma burin da ta sanya a gaba sai ba, sai an hada karfi da karfe kuma kara tabbatar da inganci, abu ne da ya karade kowanne fanni, matukar muna son kara samar da karin kudaden shiga wadanda za su yi daidai da na fadin duniya ,” , A cewar Dantsoho.
A na ta jawabin, Darakta Janar ta Kwamitin Gudanar da Muhalli na Kasuwanci na Shugaban kasa (PEBEC) Princess Zahrah Mustapha Audu ta bayyana cewa, inganganta ayyukan, za su taimaka wajen rage cunkson Jiragen Ruwa a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
A cewarta, an kaddmar da Kwamitin ne, domin a samar da sauye-sauye rashin damar da ba a samu a fannin ayyukan Tashihin da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp