Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB
Published: 6th, May 2025 GMT
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Nijeriya (JAMB) ta fitar da alƙaluman sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025, inda ta bayyana cewa yawancin daliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Litinin.                
      
				
JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar, amma cikin wannan adadi, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200.
Alƙaluman sakamakon ya nuna cewa kashi 0.63 ne na ɗalibai ƙalilan da suka samu makin da ya haura 300, wanda a jimlace suka kai ɗalibai 12,414.
A matakin maki tsakanin 250 zuwa 299 kuma, an samu ɗalibai 73,441 yayin da ɗalibai 334,560 suka samu maki tsakanin 200 zuwa 249.
Rukunin da ya fi yawan dal6ibai shi ne na maki 160 zuwa 199, inda aka samu ɗalibai dubu 983,187 wato kashi sama da 50 cikin 100 ke nan.
Haka kuma, ɗalibai dubu 488,197 suka samu maki tsakanin 140 zuwa 159, sannan dubu 57,419 suka samu tsakanin 120 zuwa 139.
Ɗalibai 3,820 kuma sun samu maki tsakanin 100 zuwa 119, sannan ɗalibai dubu 2,031 sun gaza samun ko da maki 100.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai
এছাড়াও পড়ুন:
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a Tanzaniya
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya.
A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba.
An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — TrumpRiƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.”
Baƙin da aka gayyata ne kawai aka bai wa damar halartar rantsar da Shugaba Hassan a bikin da aka haska duk da katse intanet, yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar kan sakamakon zaɓen.
An ayyana Hassan, wadda ta hau mulki a shekarar 2021 bayan rasuwar tsohon shugabanta, a matsayin wadda ta lashe zaɓen Larabar makon da ya gabata da kashi 97.66% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Sai dai ’yan hamayya sun yi watsi da sakamakon kan zargin maguɗi, suna mai cewar an yi amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima kan masu bore bayan ɓarkewar zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓen.
Hassan, mai shekaru 65, ta tsaya takara ne kawai da ’yan takara daga ƙananan jam’iyyu bayan da aka hana manyan masu ƙalubalantarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu shiga takarar.