Za A Gudanar Da Taron Tallata Fim Din “Red Silk” A Moscow
Published: 5th, May 2025 GMT
A jajibirin bikin cika shekaru 80 da samun nasarar babban yakin ceton kasa a kasar Rasha, rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, tare da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin, za su gudanar da bikin tallata fim din “Red Silk” wanda Sinawa da ‘yan Rasha suka shirya a birnin Moscow.
A matsayin sabon hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha a masana’antar fina-finai, fim din “Red Silk’ wanda aka yi hadin gwiwar shiryawa, an fitar da shi Rasha a ranar 20 ga Fabrairun wannan shekara. Kana an tsara fim din ne bisa abubuwan tarihi da suka faru a zahiri, kuma ya ba da labarin yadda ‘yan juyin juya hali na Sin da Tarayyar Soviet suka yi yaki kafada da kafada a shekarar 1927, inda suka yi nasarar raka muhimman takardu na sirri lami lafiya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Manzon Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaba Nguema Na Gabon
Bisa gayyatar da shugaban kasar Gabon Brice Nguema ya yi, Mu Hong, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, ya halarci bikin rantsuwar kama aiki na shugaba Nguema, a birnin Libreville na Gabon, a ranar Asabar da ta gabata. Kana a jiya Lahadi, shugaba Nguema na Gabon ya gana da mista Mu Hong, duk a Libreville din.
Yayin ganawarsu, Mu Hong ya ce kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa tare da kasar Gabon, da daga huldar dake tsakanin kasashen 2 zuwa wani sabon matsayi. A nasa bangare, shugaba Brice Nguema ya ce kasarsa za ta ci gaba da tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kokarin zurfafa hadin kai tare da kasar Sin a bangarori daban daban. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp