An Daure Tsohon Fira Ministan Kasar Tunisiya Shekaru 34 A Kurkuku
Published: 3rd, May 2025 GMT
Wata kotu a kasar Tunisiya ta daure tsohin fira minsitan kasar Ali al-Aridh zaman kurkuku na tsawon shekaru 34
Shi dai al-Aridhi wanda dan jami’iyyar masu kishin musulunci ta ‘al-Nahdha’ ya zama fira minista ne daga shekarar 2013 zuwa 2014.
Kotun ta zargi tsohon Fira ministan da hannu a ayyukan ta’addanci, lamarin da shi da jam’iyyar tasa su ka kore.
A cikin makwannin bayan nan dai ana yanke wa ‘yan adawa hukuncin dauri, lamarin da masu fafutuka suke dauka a matsayin bita da kulli na siyasa da shugaba Kais Sa’id yake yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine
Kasar Sin ta sake neman Amurka, da ta daina zarginta, da dora mata laifi, ya kamata kasar Amurka ta taka rawa wajen tsagaita bude wuta, da kara azama ga gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya. Jami’in ya ce, ana bukatar hadin kai wajen warware rikicin Ukraine, a maimakon rarrabuwar kawuna da yin fito-na-fito. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp