Leadership News Hausa:
2025-08-04@13:32:36 GMT

Gwamna Fintiri Ba Zai Bar PDP Ba – Humwashi

Published: 5th, May 2025 GMT

Gwamna Fintiri Ba Zai Bar PDP Ba – Humwashi

Kakakin Gwamnan Jihar Adamawa, Humwashi Wonosikou, ya ƙaryata jita-jitar cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na shirin barin jam’iyyar PDP, yana mai cewa shugaban jihar ya cikin jam’iyyar kafada daram.

A wata hira da manema labarai a Yola, Wonosikou ya bayyana cewa Gwamna Fintiri ya mai da hankali kan ayyukansa na shugabancin kwamitin taron jam’iyyar PDP, ba shirin komawa wata jam’iyya ba.

“Gwamna Fintiri ɗan PDP ne kwarai. Ba zai bar jam’iyyar ba,” in ji shi.

An Maka Gwamna Fintiri A Gaban Kotu Kan Ƙirƙiro Sabbin Masarautu A Jihar Adamawa  Babu Dalilin Da Zai Sanya Wasu Mambobin PDP Ficewa A Jam’iyyar A Bauchi

Labarin ya zo ne a lokacin da wasu manyan ‘yan PDP ke komawa jam’iyyar APC, kamar yadda Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi tare da tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa da dukkan tsarin PDP a jihar.

Shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyyarsa tana sa ran samun ƙarin gwamnonin PDP da za su shigo cikinta. Taron ya kuma yi nazari kan nasarorin gwamnatin Fintiri a cikin shekarar 2025.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Adamawa Gwamna Fintiri

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Manyan Matakan Kare Jihar Daga Ambaliyar Ruwa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al’umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana.

Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya bayyana haka yayin da yake duba aikin jingar ruwan kogi da ya ratsa garuruwan Auyo da Tsidir da Agin da Matsa da Sorakin da Jiyan da Tage da Turabu da kuma Tandanu.

Alhaji Hamza Hadejia ya ce daga zuwan Gwamna Umar Namadi kan karagar mulkin Jihar, ya dauki kwararan matakai don kaucewa ambaliyar ruwa, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma bayyana cewar, Gwamna Namadi ya inganta harkar noma don tabbatar da isasshen abinci da samar da ayyukan yi ga al’ummar karkara.

A cewar sa, kwamitin fasaha na magance ambaliya ya zage damtse wajen sarrafa koguna da gina kwarya-kwaryar shinge a wuraren da ake sa ran ambaliya domin magance matsalar.

A don haka, Hamza Muhammad Hadejia, ya bukaci jama’a su ci gaba da bada hadin kai da goyon baya ga gwamnatin jihar domin a cimma wannan manufa domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyon bayan da ya ke baiwa ayyukan kwamitin a kowane lokaci.

A jawaban su, Dagacin Turabu Malam Shu’aibu Saje da Shugaban ci gaban al’umma Sani Barde da tsohon kansila Umar Jiyan, sun jinjinawa Gwamna Umar Namadi da shugaban karamar hukumar Auyo da mai ba da shawara Hamza Hadejia bisa kokarin kare rayuka da dukiyoyin su, tare da tabbatar da gudunmawar su don cimma burin gwamnati kan magance ambaliya a yankin.

Sun kuma godewa gwamnatin jihar Jigawan da ta kananan hukumomi bisa samar da ababen more rayuwa da kuma bunkasa harkokin ilimi da lafiya da ruwa da wuta da hanyoyi da kuma bunkasa noma don samar da isasshen abinci da ayyykan yi a tsakanin al’ummomin karkara.

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa
  • Gwamnan Neja Ya Bada Umarnin Sake Bude Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai.
  • Gwamnan Jihar Kwara Ya Hori Sabbin Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima Akan Kishin Kasa
  • Gwamna Abdulrazaq Ya Duba Titi Mai Tsawo Kilomita 49
  • Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Manyan Matakan Kare Jihar Daga Ambaliyar Ruwa
  • Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi
  • Gwamna Fintiri Ya Karrama Kocin Super Falcons, Madugu Da Naira Miliyan 50
  • Sauya Sheƙa: Sanatoci Biyu APC Ke Buƙata Wajen Samun Kashi Biyu Cikin Uku A Majalisar Dattawa
  • HOTUNA: Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gudi na Yobe bayan rasuwarsa a Abuja
  • PDP ta mutu murus a Kano — Shugaban NNPP